Dalilin Da Yasa Gwamnonin Arewa Suka Marawa Tinubu Baya a Zaben 2023, Masari

Dalilin Da Yasa Gwamnonin Arewa Suka Marawa Tinubu Baya a Zaben 2023, Masari

  • Gwamnan Katsina ya bayyana ainihin dalilin da yasa gwamnonin arewa suka marawa Bola Tinubu baya a zaben 2023
  • Aminu Bello Masari, ya ce Allah ne ya ceci jam'iyyar APC daga kunyata har ta samu gagarumar nasara a babban zaɓe
  • Ya kuma kara da cewa rashin bin tsarin karba-karba ne ya jefa wasu jam'iyyun adawa cikin rikici

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya tono asalin dalilin da ya sa gwamnonin arewa suka goyi bayan takarar zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Gwamnan ya bayyana dalilinsu yayin da ya je ziyarar bankwana fadar Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq-Umar, ranar Alhamis, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gwamna Aminu Bello Masari.
Dalilin Da Yasa Gwamnonin Arewa Suka Marawa Tinubu Baya a Zaben 2023, Masari Hoto: Bashir Ya'u/facebook
Asali: Facebook

A cewar gwamna Masari, gwamnonin arewa na jam'iyyar APC sun marawa Tinubu baya domin girmama tsarin karba-karɓa na jam'iyya mai mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Yi Hasahen Wanda Zai Samu Nasara a Kotu Tsakanin Tinubu da Atiku, Ya Faɗi Hujja

Masari ya ƙara da cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Allah ne ya cece mu daga kunyata a zaben da aka kammala a ƙasar nan, jam'iyyarmu APC ta samu nasara. Ya kamata duk mai hangen nesa ya gode wa Allah saboda da APC ba ta ci zaɓe ba, mutane zasu yi tunanin bamu raɓuka komai ba."
"Koma menene makircin da wasu suka ƙullawa ƙasar nan, Allah ya taimaki shugaba Muhammadu Buhari, ya kare gaskiyarsa, domin da kashi muka sha, shi za'a fara ɗorawa laifi."
"Duk mai tunani ya hango haka, musamman mu gwamnonin arewa na APC, mun ga yunkuri kala-kala na ɓata wa Buhari suna. Duk wata jam'iyya ta yarda da tsarin karba-karba, wasu basu so ba amma muka ce haka za'ai."

Abinda ya ruguza wasu jam'iyyun adawa - Masari

Gwamnan ya ƙara da cewa rashin bin tsarin karba-karba a wasu jam'iyyun adawa ne ya jefa su cikin rigingimu wanda har yanzu ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa.

Kara karanta wannan

Shugabancin Majalisar Dattawa: Yari, Kalu da Musa Sun Kai Kokensu Wurin Adamu

A rahoton PM News, Gwamna Masari ya ce:

"Saboda haka tunda mun san mun yi haka (tsarin karba-karba), Allah ya san halin da ƙasarmu ke ciki a halin yanzu amma ya kamata mu tsaya tsayin daka kan alkawurran da muka ɗauka."
"Wannan ne ya sa ake ganin girman 'yan arewa kuma suke cin nasara, saboda idan har mun ce Eh, to ko za'a kai ruwa rana muna nan a kan Eh a kowane lokaci."

Tambuwal ya sa ran samun nasarar Atiku a Kotu

A wani labarin kuma Gwamna Tambuwal Ya Yi Hasahen Hukuncin da Kotu Zabe Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato ya bayyana kwarin guiwar cewa Kotu zata maida wa Atiku haƙƙinsa na zama shugaban ƙasa mai jiran gado.

A wurin taron da PDP ta shirya wa gwamnoni masu jiran gado, Tambuwal ya ce alamu sun nuna narasa zata dawo hannun tsohon mataimakin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Asali: Legit.ng

Online view pixel