Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

  • Kotun koli a Najeriya ta ce babu wata doka da ta tilastawa hukumar zaɓe INEC dora sakamako kan shafinta na yanar gizo
  • Wannan hukunci ya yi daidai da hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Abuja a Kes ɗin da ya kunshi Peter Obi da Bola Tinubu
  • Alkalan Kotunan biyu sun yanke cewa INEC ke da ikon zaben hanyar da zata bi wajen tattara sakamakon zaɓe

Abuja - Kotun Ƙoli ta ayyana cewa ba dole bane hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta yi amfani da Intanet wajen tattara sakamakon zaɓe.

Kotun ta faɗi haka ne ranar Talata, 9 ga watan Mayu, 2023 yayin da take yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola, ya shigar.

Na'urar BVAS.
Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet Hoto: @thecableng
Asali: UGC

Kwamitin alƙalai biyar na Kotun Allah ya isa ya jaddada cewa babu wata doka da ta tanadi cewa baturen zaɓe na mazaɓa ya tura adadin masu kaɗa kuri'a da na'urar BVAS ta tantance zuwa ma'ajiyar bayanan INEC.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabon Babban Mai Ba Da Shawara Kan Tsaro a Najeriya

A rahoton The Cable, shugaban kwamitin Alkalan wanda ya karanta hukuncin Kotun ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda haka korafin mai kara cewa dole baturen zaben mazaɓa ya aika adadin mutanen da na'aurar BVAS ta tantance nan take zuwa ma'adanar bayanan INEC ba shi da madogara."

Tasirin da wannan hukuncin zai yi

Masu sharhi kan harkokin siyasa sun ce tasirin da wannan hukuncin zai yi shi ne duk wata ƙara da mai yuwuwa nan gaba za'a kai gaban Kotu kan gaza tura sakmako ta intanet ba zata kai labari ba.

Idan baku manta ba gazawar INEC wajen tura sakamko kai tsaye ta yanar gizo na ɗaya daga cikin ƙorafin da Peter Obi na LP ya kalubalanci nasarar Bola Tinubu a gaban Kotu.

A cewar Obi, gazawar INEC ta dora sakamakon zabe a kan shafin da ta ware IREV a ranar da yan Najeriya suka kaɗa kuri'a ya rushe baki ɗaya zaben.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Kotun Koli Ta Bayyana Sahihin Wanda Ya Ci Zaben Gwamnan Osun

Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Da Shawara Kan Tsaro

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Naɗa Sabon Babban Mai Ba Da Shawara Kan Tsaro a Najeriya

Kwanaki kaɗan gabanin karewar wa'adinsa, Shugaba Buhari, ya naɗa sabon SSA kan harkokin yan sandan ƙasa da ƙasa da yaki da ayyukan ta'addanci

Buhari, wanda zai miƙa wa zababben shugaban ƙasa mulki ranar 29 ga watan Mayu, ya ce wannan naɗin zai taimakawa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel