Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Da Shawara Kan Tsaro a Najeriya

Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Da Shawara Kan Tsaro a Najeriya

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa AIG Garba Baba Umar a matsayin SSA a ofishin ministan kula da harkokin 'yan sanda
  • Fadar shugaban ƙasa ta ce hakan zai baiwa AIG Umar damar karisa zangonsa a matsayin mamban kwamitin zartaswa na INTERPOL
  • Wannan naɗi zai fara aiki ranar 16 ga watan Mayu yayin da wa'adinsa a INTERPOL zai kare a watan Nuwamba, 2024

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, ranar Alhamis, 11 ga watan Mayu, ya naɗa mataimakin sufetan yan sanda (AIG) wanda ke dab da ritaya, Garba Baba Umar, a matsayin babban mai ba da shawara kan tsaro (SSA).

Buhari ya naɗa AIG Umar a matsayin mashawarci kan harkokin tsaron fannin hukumar 'yan sandan ƙasa da ƙasa (INTERPOL) da yaƙi da ayyukan ta'addanci a Ofishin Ministan jin daɗin yan sanda.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Yi Hasahen Wanda Zai Samu Nasara a Kotu Tsakanin Tinubu da Atiku, Ya Faɗi Hujja

AIG Umar da Buhari.
Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Mai Ba Da Shawara Kan Tsaro a Najeriya Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A cewar fadar shugaban kasa, Umar ya samu wannan muƙami ne domin Najeriya ta ci gaba da riƙe muhimmin muƙami da kuma shi kansa ya samu damar ƙarisa zangon mulki a matsayin mamban INTERPOL.

Cikakken bayanin wannan sabon naɗi

Yayin rattaba hannu kan naɗin, Buhari ya yi waiwayen yadda gwamnarin tarayya ta rike tsohin zaɓaɓɓen mamba, AIG Kamal Subair (mai ritaya) duk da ya yi ritaya a 2018.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan Shugaba Buhari ya bayyana cewa a tsawon lokacin da ya kasance a matsayin cikakken mamban kwamitin zartaswan INTERPOL, AIG Umar, ya taimaka wa Najeriya ta hanyoyi da dama.

A cewarsa, ana fatan zai yi abinda ya zarce haka a bangaren harkokin iyaka, yaƙi ta'addanci da kawo karshen aikata muggan laifuka da taimaka wa yan Najeriya su samu muƙamai a INTERPOL.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Kai Ziyarar Bankwana Fadar Sarakuna 2, Ya Nemi Talakawa Su Yafe Masa Kura-Kuransa

Zangon mulkin AIG Umar a hukumar INTERPOL zai kare ne a watan Nuwamba, 2024 kuma sabon naɗin da shugaban ƙasa ya masa zai fara aiki ranar 16 ga watan Mayu, 2023.

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

A wani labarin kuma Kotun koli a Najeriya ta ce babu dokar da ta tilasta tura sakamakon zaɓe ta Internet kai tsaye daga rumfunan zaɓe

Kotun ta yanke wannan hukunci ne ranar Talata, 9 ga watan Mayu, 2023 yayin da take raba gardama kan takaddamar zaben gwamnan jihar Osun

A cewar alkalin Kotun, ba bu wata doka da ta tanadi cewa wajibi ma'aikatan zabe su tura sakamako daga rumfuna zuwa majiyar bayanan INEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel