Buhari: Abin da Ya Sa Na Ki Fitowa Karara In Goyi Bayan Magajina a Zaben Gwanin APC

Buhari: Abin da Ya Sa Na Ki Fitowa Karara In Goyi Bayan Magajina a Zaben Gwanin APC

  • Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya dawo da maganar zaben ‘dan takaran shugaban kasa da aka yi a APC
  • Shugaban na Najeriya mai barin gado ya ce babu dalilin da zai fifita wani daga cikin masu neman takara
  • Buhari yana ganin tun da damukaradiyya ta ke aiki, a bar wanda ya iya allonsa ya wanke a jam’iyya

Nasarawa - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce da gangan ya ki yarda ya nuna wanda ya ke so a zaben tsaida gwanin shugaban kasa na APC.

Muhammadu Buhari ya nuna babu adalci idan ya ba wani mai neman takara fifiko a tsarin damukaradiyya, The Nation ta kawo wannan rahoto dazu.

Mai girma shugaban na Najeriya ya ce ya nemi shugabancin Najeriya sau uku amma duk ya kare a kotu, don haka ba zai iya daga hannun magajinsa ba.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan Majalisa Sun Fadi Wanda Suke Goyon Baya Ya Zama Sabon Shugaba

A zaben fitar da ‘dan takara da jam’iyyar APC ta shirya, shugaban kasar bai yi karfa-karfa ba.

Bai goyi bayan kowa ba

Buhari bai nuna wanda yake sha’awar ya samu takara a APC tsakanin irinsu Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da kuma Ahmad Lawan ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Muhammadu Buhari ya tunawa al’umma yadda Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello ya tabbatar da adalci da gaskiya a lokacin da yake Firimiyan Arewa.

Buhari
Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

An tuna da Ahmadu Bello

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a wajen taron da gwamnatin Nasarawa da gidauniyar Ahmadu Bello suka shirya domin tunawa da Firimiya.

Vanguard ta ce Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya wakilci Buhari a wajen taron da aka yi garin Lafia a Nasarawa.

A madadin mai gidansa, Ibrahim Gambari ya yi kira ga mutanen Najeriya su karbi sakamakon zabukan da aka yi, ya ce duk masu ta-cewa su tafi kotu.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran da Ake Zargi da Yi wa APC Aiki a 2023 Ya Fito Fili Yana Goyon Bayan Tinubu

Wanda aka gayyato domin ya zama mai jawabi shi ne Farfesa Patrick Lumumba daga kasar Kenya, Simon Bako Lalong ma ya tofa albarkacin bakinsa.

Rahoton ya ce taron ya samu halartar tsofaffin Gwamnoni; Babangida Aliyu, Murtala Nyako, Idris Abubakar, Tanko Al-Makura sai Abdullahi Adamu.

Sai Tajudeen Abbas ya yi da gaske

An ji labari Tajudeen Abbas zai fuskanci Ahmed Idris Wase, Muktar Betara Aliyu da Yusuf Adamu Gagdi da wasu abokan aikinsa wajen shugabancin majalisa.

‘Dan majalisar mazabar Zaria da kewaye yana da jan aiki a gabansa a takarar da za ayi a watan Yuni domin babu tabbacin ‘yan takaran APC za su janye masa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel