Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki

Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki

  • A cikin hikimar da ya saba, Shehu Sani ya bada wasu shawarwari ga wadanda za su karbi mulki
  • Tsohon ‘dan majalisar kasar ya yi wani gajeren rubutu a dandalin Facebook mai daukar hankali
  • Sanata Shehu Sani ya ankarar da shugabanni masu jiran gado a kan yadda za su kula da fadarsu

Abuja - Shehu Sani ‘dan siyasa ne wanda kuma ya yi suna wajen gwagwarmaya a Najeriya, ya kan tofa albarkacin baki a kan sha’anin kasa.

Yayin da ake shirin karbar mulki, an ji fitaccen ‘Dan siyasar ya yi wasu maganganu na azanci a shafinsa na Facebook a matsayin shawarwari.

Kwamred bai kama suna ko mukamin wadanda yake ba shawara ba, amma ya nuna cewa kira ne ga wadanda za su rike madafan iko a Abuja.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Abin da Ya Hana Kwankwaso Zuwa Kotu a Kan Zaben Shugaban Kasa

Sanata Sani Shehu ya bada shawarar ne a bulus, ma’ana kyauta ba tare da an tambaye shi ba.

Sai an yi hattara a mulki

Daga cikin abin da wannan shawara ta kunsa shi ne wanda zai dare kujerar mulki ya yi hattara da makiya da kuma na-kusa da masu barin ofis.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika tsohon Sanatan na Kaduna ya ankarar da wadanda za su karbi shugabanci a kan wasu boyayyu da ke rike da madafun iko.

Shehu Sani
Sanata Shehu Sani a Majalisa Hoto: @senatorshehusani
Asali: Facebook

Kamar yadda ya rubuta a Facebook, Sanata Sani ya nuna akwai wadanda ba don Allah za su shigo fadar mai mulki ba, ya doke ‘dan takaransu ne.

Idan kunne ya ji...jiki ya tsira

"Shawara a bulus ga sabon mai mulki da za ayi a Abuja:
Ka da ka gaji na-hannun daman shugaba mai barin gado, kai ma za su ci amanarka.

Kara karanta wannan

Kujerar Kakaki: Ado Doguwa Ya Ce Mata 4 Da 'Ya'ya 28 Yake Dashi, Zai Iya Ji da Majalisa

Ka da ka gaji makiyan shugaba mai barin gado, kai ma za su yake ka.
Ka da ka gaji masu juya akalar gwamnatin shugaba mai barin gado, kai ma za su juya ka.
Ka sa ido a kan wadanda suka shigo fadarka alhali ba kai ne asalin zabinsu na farko ba.
Ka fi maida hankali a game da abin da suka fada da harshensu, ba da Ingilishi ba."

- Shehu Sani

HYPREP ya yi sabon shugaba

A ranar Larabar nan ne rahoto ya zo cewa fadar shugaban Najeriya ta bada sanarwa cewa an yi waje da wanda yake jagorantar aikin HYPREP.

An sanar a Twitter cewa Farfesa Nanibarini Zabbey zai dare kujerar shugaban HYPREP ba tare da bata lokaci ba, ya canji Dr. Ferdinand Giadom

Asali: Legit.ng

Online view pixel