Yawaita Cin Bashi a Sokoto: Za a Binciki Gwamnatin Tambuwal Bayan Karewar Wa’adinsa

Yawaita Cin Bashi a Sokoto: Za a Binciki Gwamnatin Tambuwal Bayan Karewar Wa’adinsa

  • Zababben gwamnan jihar Sokoto ya sha alwashin binciken binciken gwamnatin Aminu Tambuwal game da basuka
  • Ahmed Idris ya tabbatar da hakan ne don samun sanin inda gwamnatinsa za ta dosa cikin kasa da wata daya da ya rage kafin rantsarwa
  • Kwamitin wanda ya kunshi mambobi 20, an kafa shi ne don binciko badakalar basukan da gwamnatin ta ci

Jihar Sokoto - Zababben gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu ya kafa kwamitin kudade da tantance basuka don binciken gwamnati mai barin gwado ta gwamna Aminu Waziri Tambuwal, Daily Trust ta rahoto.

An zabi Ahmed Aliyu ne a karkashin tutar jamìyyar APC wadda itace babbar jam`iyyar adawa a jihar, bayan jam`iyyar PDP ta shafe shekaru tana mulkin jihar.

Tambuwal
Zababben gwamnan jihar Sokoto zai bincike Tambuwal bayan karewar wa'adinsa. Hoto: Premium Times.
Asali: UGC

Kwamitin da zababben mataimakin gwamnan jihar Mohammed Idris Gobir ke jagoranta zata yi aiki ne don bankado dukkan basukan da gwamnatin Tambuwal ta runtumo tun farkon hawanta.

Kara karanta wannan

Assha: Shugaban APC ya ce gwamnan Arewa bai iya komai ba, 'yan sanda sun kwamushe shi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sannan kwamitin zai binciko da tabbatar da cewa basukan da aka ciwo anyi amfani dasu ta hanyar da ya dace, da bayyan dalilin karban basukan da kuma yawansu don samun bayanai wurin bincike.

Yaushe aka kaddamar da kwamitin?

Shugaban kwamitin, Ambasada Abubakar Sani ya kaddamar da kwamitin ne a ranar Laraba 3 ga watan Mayu wanda ya kunshi mambobi 20.

Wasu `yan majalisar jihar na zargin cewa gwamnatin ta karbo basukan kudade fiye da N86bn, kafar labarai ta Solace Base ta tattaro.

Akan samu rashin jituwa da zargin juna tsakanin gwamnoni masu barin gado da kuma zababbu a jihohin daban-daban na Najeriya.

Al'amari irin wannan yanzu haka yana faruwa a Kano, gwamna Ganduje na musayar kalamai da bangaren gwamna mai jiran gado Abba Kabir Yusuf.

Na kawo masarautun Kano don su zauna

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Yi Manyan Nade-Nade Masu Muhimmanci a Gwamnatinsa Yan Makonni Kafin Mika Mulki

A wani labari, gwamna Abdullahi Umaru Ganduje a Kano ya ce ya kafa masarautun Kano ne domin su tsaya daram ba mai iya ture su da izinin Allah.

Ya fadi hakan ne a ranar ma'aikata ta Najeriya lokacin da yake yiwa Kwankwaso martani kan maganar da ya yi game da masarautun Kano da yiwuwar gyara su.

Ya ce, ya karkasa masarautun Kano ne domin kawo ci gaba da kuma tabbatar da an mutunta dukkan mazauna garuruwa biyar da aka ba babbar masarauta a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel