Tambuwal Ya Nada Sabbin Sakatarorin Din-din-din Da Daraktoci 38 Yan Makonni Kafin Mika Mulki

Tambuwal Ya Nada Sabbin Sakatarorin Din-din-din Da Daraktoci 38 Yan Makonni Kafin Mika Mulki

  • Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yi sabbin nade-nade yan kwanaki kafin barinsa mulki ga sabuwar gwamnati mai kamawa
  • Tambuwal ya nada sabbin sakatarorin din-din-din guda 23 da kuma manyan daraktoci 15
  • A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da sabon zababben gwamnan jihar Sokoto

Sokoto - A ranar Talata, 2 ga watan Mayu, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya rantsar da sabbin sakatarorin din-din-din 23 da manyan daraktoci 15, jaridar Daily Trust ta rahoto.

An gunadar da bikin rantsarwar kwanaki 27 kafin mika mulki ga sabon zababben gwamnan jihar.

Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoo
Tambuwal Ya Nada Sabbin Sakatarorin Din-din-din Da Daraktoci 38 Yan Makonni Kafin Mika Mulki Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Daga cikin wadanda aka nada akwai babban hadiminsa da daraktan labarai na ofishin mataimakin gwamna Abdulnaseer Abubakar Sayinna da Aminu Abubakar.

Kungiyar kwadago reshen jihar Sokoto ta koka kan rashin biyan albashi a kan kari

Kara karanta wannan

Rigima Ta Ɓalle, Yan Sanda Sun Mamaye Majalisar Dokokin Jihar da PDP Ke Mulki

Nadin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Sokoto ta koka kan jinkirin da aka samu wajen biyan albashi, rahoton The Eagle.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kungiyar kwadagon ta kuma caccaki gwamnatin Tambuwal kan rashin tura wa kungiyoyin kwadago da na hadin gwiwar ma'aikata kudaden da ake cirewa daga albashin ma’aikatan.

Hakazalika, kungiyar ta kuma koka cewa har yanzu biyan kudaden fansho da hakkokin ma'aikatan gwamnati da suka yi ritaya ya kasance babban kalubale a jihar.

Arewa ta cancanci shugabancin majalisar dattawa, Yari

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma zababben sanata a zaben 2023, Abdul'azeez Yari ya bayyana cewar yankin arewacin Najeriya ya cancanci a mika masa kujerar shugabancin majalisar dattawa ta 10.

Yari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 30 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Fara Shirye-shiryen Cefanar da Asibitin Fadar Shugaban Kasa

Ya bayyana cewar bai kamata jam'iyyar APC ta yi la'akari da addini ko kabilanci wajen rabon mukamai a majalisar ba kuma cewa arewa ta yi namijin kokari a nasarar da jam'iyyar mai mulki ta samu a zaben da aka yi.

Zababben sanatan yana daya daga cikin yan majalisar tarayya da ke neman takarar kujerar ta shugaban majalisar dattawa a majalisa ta goma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel