Barka da Sallah: Babban Abinda Na Yi Dana Sani a Mulkina, Ministan Abuja

Barka da Sallah: Babban Abinda Na Yi Dana Sani a Mulkina, Ministan Abuja

  • Ministan Abuja, Mallam Muhammed Bello, ya faɗi babban abinda yake dana sani a zamanin mulkinsa
  • Yayin da ya je yi wa Buhari barka da Sallah, Bello ya ce ya yi yunkurin jawo hankalin Sanata Aduda ya sauya sheƙa zuwa APC
  • Sanata Aduda, ya yaba wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bisa iya jure kowa har da jam'iyyar adawa

Abuja - Ministan birnin tarayya Abuja, Muhammed Bello, ya ce babban abinda yake dana sani shi ne gaza jawo ra'ayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Philip Aduda, daga PDP ya koma APC.

Ministan ya bayyana haka ne yayin da kaiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ziyarar barka da Sallah a fadar shugaban ƙasa ranar Jummu'a, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Barka da sallah.
Barka da Sallah: Babban Abinda Na Yi Dana Sani a Mulkina, Ministan Abuja Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Mista Bello ya ce ya yi yunkurin dawo da Sanata Aduda cikin inuwar jam'iyyar APC amma kokarinsa ya tashi banza tun gabanin Ambaliyar Labour Party ta yi awon gaba da shi ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Ɗumi: Shugaba Buhari Ya Tona Asirin Wani Gwamnan Arewa Wanda Ya Sha Kaye a Zaɓen 2023

Sanata Aduda, wanda ke wakiltar birnin tarayya Abuja a majalisar dattawa, kuma mamban jam'iyyar PDP ya sha kashi hannun ɗan takarar Labour Party, Ireti Kingibe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mohammed Bello ya ƙara da cewa tunda shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawan Najeriya ya rasa kujerarsa ga LP, ya kamata ya yi nazari ya duba yuwuwar sauya sheƙa zuwa APC.

Ministan ya ayyana Sanata Aduda a matsayin mai gida gada duk da kuwa ya kasance ɗan jam'iyyar adawa

Bayan haka Bello ya ba da shawari cikin raha cewa ya kamata a tura Sanatan zuwa ƙasar Ukraine a matsayin ambasada tun da a yanzu ƙasa da mako shida ya rage masa a kujerar Sanata.

Da yake na sa jawabin, Sanata Aduda ya yaba wa shugaban kasa Buhari bisa haƙuri da juriya ga matsin lambar kowa har da jam'iyyar adawa.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Hana Buhari Tsoma Baki a Tirka-Tirkar Binani da Fintiri – Gwamnatin Tarayya

Bugu da ƙari kuma ya ce zai yi tunani kan gayyatarsa zuwa jam'iyyar APC mai mulki da Ministan Abuja ya yi.

INEC ta sake magana kan REC ɗin Adamawa

A wani labarin kuma Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Gudu Ba'a San Inda Ya Buya Ba

Hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta ce har yanzun ba ta ga keyar kwamishinan zaben jihar Adamawa ba tun da ya yi azarɓaɓin ayyana sakamakon zaɓe ba kan ƙa'ida ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel