Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Gudu Ba'a San Inda Ya Buya Ba, INEC

Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Gudu Ba'a San Inda Ya Buya Ba, INEC

  • INEC ta ce har yanzun ba ta ga keyar dakataccen kwamishinan zaɓen jihar Adamawa ba tun da ya aikata laifi
  • Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai ya ce INEC ta aike masa da sakon ya zo Abuja tun ranar Lahadi amma har yau shiru
  • Ya ce hukumar yan sanda ke da ikon ayyana nemansa ruwa a jallo idan buƙatar hakan ta taso

Abuja - Kwamishinan hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) na jihar Adamawa (REC), wanda aka dakatar, Barista Hudu Yunusa Ari, ya ɓace ɓat babu wanda ya san inda ya shiga.

Kwamishinan yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a na INEC ta ƙasa, Festus Okoye, ne ya faɗi haka yayin hira da Channels tv cikin shirin Sunrise Daily ranar Jummu'a.

Barista Hudu Ari.
Dakataccen Kwamishinan Zaben Adamawa Ya Gudu Ba'a San Inda Ya Buya Ba, INEC Hoto: channelstv
Asali: UGC

A ranar Lahadin da ta shige, Ari ya haddasa ruɗani sa'ilin da ya bayyana sakamakon ƙarishen zaɓen gwamnan jihar Adamawa duk da ba'a kammala tattarawa ba.

Kara karanta wannan

Fintiri Vs Binani: INEC Ta Baiwa Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Adamawa Shaidar Samun Nasara

Ya take doka wajen ayyana Sanata Aishatu Ɗahiru Ahmed, wacce aka fi sani da Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Adamawa. Nan take INEC ta soke sanarwan ta kira shi zuwa Abuja.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ina kwamishinam zaɓen ya buya?

Yayin wannan hira da Daily Trust ta bibiya, Mista Okoye ya ce:

"Bamu san inda ya shiga ba saboda bayan abinda ya aikata, mun tura masa wasiƙa kuma mun kira lambar wayansa, bai biyo kowane kira ba kuma bai ɗaga ko ɗaya ba."
"Mun buƙaci ya kawo kansa hedkwatar INEC ranar Lahadi amma bamu ga ƙeyarsa ba. Mun ƙara aika masa ya zo ranar Litinin, bai zo ba. Har kawo yanzu bamu san inda ya shiga ba kuma bai ɗaga kiran da aka masa ba."

Dangane da ko za'a ayyana neman Ari ruwa a jallo matuƙar bai amsa kiran INEC ba, Kwamishinan ya bayyana cewa wannan ya rataya ne a wuyan rundunar 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Sanar Da Lokacin Ba Fintiri Satifiket Din Lashe Zaben Gwamna

"Eh wannan yana hannun hukumar 'yan sanda, idan suna buƙatar ganinsa dole lokacin bincike kuma aka neme shi aka rasa, to daga nan ne zasu duba yuwuwar ayyana nemansa ruwa a jallo."

A wani labarin kuma Jerin Yan Takarar Gwamna a Inuwar APC, PDP da Labour Party a Jihar Bayelsa

Hukumar zaɓe ta sanya ranar zaben gwamna a wasu jihohin Najeriya uku waɗanda zaɓensu ba ya cikin lokacin babban zaɓe.

Jihar Bayelsa na ɗaya daga cikin jihohin kuma tuni manyan jam'iyyu suka tsayar da waɗanda zasu kara a zaben da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel