Mataimakin Shugaban APC Ya Fasa Kwai Kan Yadda Ake Bayar Da Cin Hanci Don Samun Shugabancin Majalisa

Mataimakin Shugaban APC Ya Fasa Kwai Kan Yadda Ake Bayar Da Cin Hanci Don Samun Shugabancin Majalisa

  • Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya fasa kwai kan yadda masu neman shugabancin majalisa ke bayar da na goro
  • Salihu Lukman yace akwai matsala yadda masu neman shugabancin suka koma bayar da cin hanci
  • Yayi kira ga shugabannin jam'iyyar da su tashi tsaye haiƙan domin kawo ƙarshen wannan rashin gaskiyar

Abuja - Mataimakin shugaban jam'iyyar All All Progressives Congress (APC) na ƙasa, na yankin Arewa maso Yamma, Salihu Moh. Lukman, ya fasa kwai kan abinda masu neman shugabancin kujerar majalisa ta 10 suke yi.

Salihun Lukman ya zargi masu neman shugabancin majalisar ta 10 da bayar da cin hanci ga kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam'iyyar APC.

Lukman
Mataimakin Shugaban APC Ya Fasa Kwai Kan Yadda Ake Bayar Da Cin Hanci Don Samun Shugabancin Majalisa Hoto: Blueprint
Asali: UGC

Mataimakin shugaban jam'iyyar yayi wannan zargin ne a wata ƴar gajeruwar tattaunawa da jaridar Vanguard, ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

To fah: Matasan Arewa sun fadi wadanda suke so su zama shugabannin majalisa

Wannan zargin na Lukman yana zuwa bayan rahotanni sun bayyana cewa ƴan majalisun dake neman kujerar shugabancin majalisun tarayya sun fara mayar da sakatariyar jam'iyyar wajen ajiyar kaya inda aka ga manyan motoci,

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Suna sauke shinkafa da sukari domin rabawa shugabannin jam'iyyar da ƴan kwamitin NWC, Rahoton Blueprint

A kalamansa:

“Ina son nayi kira zuwa ga shigabannin mu da abokan aikina na NWC. Yakamata mu dauƙi dukkanin matakan da suka dace domin kawar da yin ba daidai ba a jam'iyyar mu."
"Yadda abubuwa suke a yanzu abin damuwa ne yadda mutanen dake neman shugabancin majalisa suke bibiyar mambobin NWC ta hanyar da bata dace ba. Bana tunanin hakan ya dace."
"Aƙalla sanatoci biyu, abin takaici daga yanki na waɗanda suke neman shugabancin majalisar dattawa sun sun aiko da buhunan shinkafa da sukari."
“Wani mamba na majalisar wakilai shima daga yanki na wanda yake neman kakakin majalisa, na fahimci ya turawa ƴan NWC daban-daban buhunan shinkafa."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bayan PDP, Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa da Wasu Shugabanni 3

Ya cigaba da cewa:

"Har ya zuwa yau bamu yanke hukunci ba kan rarraba ofisoshin a jam'iyya ba. Ina tunanin bai dace ba shugabanni a matakin da muke yanzu suna yin irin wannna aikin rashin gaskiyar ba."
“I na ganin cin fuska ne ayi tunanin cewa za a iya toshe mana baki da cin hanci. Ina ganin yakamata shugabannin mu musamman shugaban jam'iyya da sakataren sa su tashi tsaye wajen hana wannan rashin gaskiyar."
"Saboda idan da basu bayar da izni ba, ban san meyasa buhunan shinkafa da sukari zasu isa har sakatariyar jam'iyyar ba har a kai ga rarraba su."

"Sun Fara Siyan Ta Da Kudi" Sanatan APC Ya Magantu Kan Shugabancin Majalisa Ta 10

A wani labarin na daban kuma, sanatan APC ya tono wata ƙulla-ƙulla da ake yi domin samun shugabancin majalisa ta 10.

Sanata Ali Ndume yace an fara wasa da kuɗi domin siyan shugabancin majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel