Abba Kabir Yusuf Ya Kafa Kwamitin Mutum 65 da Zai Karbi Mulki a Hannun Ganduje

Abba Kabir Yusuf Ya Kafa Kwamitin Mutum 65 da Zai Karbi Mulki a Hannun Ganduje

  • Abba Kabir Yusuf ya nada kwamitin da zai yi aikin karbar mulki daga hannun Abdullahi Umar Ganduje
  • A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Abba Gida Gida zai gaji Dr. Abdullahi Umar Ganduje a jihar Kano
  • Jigo a NNPP, Dr. Abdullahi Baffa Bichi shi ne shugaban kwamitin da yake kunshe da mutane fiye da 60

Kano - A yau Juma’a, Abba Kabir Yusuf ya fitar da sunayen wadanda za su yi aiki a kwamitin da zai karbi mulki daga hannun Abdullahi Umar Ganduje.

Zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya fitar da wannan sanarwa a shafinsa na Facebook da Twitter da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa.

Daily Trust ta ce tsohon shugaban hukumar TETFund, Dr. Abdullahi Baffa Bichi ne zai jagoranci kwamitin, sai kuma Abdullahi Musa shi ne Sakatare.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Yi Nadin Mukamin Farko Bayan Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kano

Kwamitin mai dauke da mutane 65 zai yi aikin shirin karbar shugabanci daga hannun Gwamnatin Mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje a Mayu.

Gobe kwamiti zai soma aiki

Sanarwar ta ce za a rantsar da kwamitin ne a ranar Asabar, 1 ga watan Afrilu da karfe 2:00 na rana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce daga baya za a fitar da sunayen ‘yan kananan kwamitin da za su yi wa Abba Gida Gida shirin kafa gwamnati a Kano.

Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdussalam Hoto: @salisuyahayahototo
Asali: Facebook

Su wanene 'yan kwamitin?

Tsohon gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafizu Abubakar yana cikin ‘yan gaba-gaba a kwamitin, sannan akwai tsohon shugaban PDP, Shehu Wada Sagagi.

A kwamitin akwai shugaban NNPP, Umar Haruna Doguwa da tsohon ‘dan takarar Gwamna a Kano, Hon. Ahmad Garba Bichi da Sheikh Aminu Daurawa.

Har ila yau an sa sunayen Dr. Ali Haruna Makoda, Haruna Dederi, Farfesa Sani Lawan Malumfashi, Farouk Kurawa, da Dr. Aminu Garba Magashi.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan 2023: Taya Murnar Nasir Yusuf Gawuna Ga Abba Kabir Yusuf Gida-Gida

A jerin akwai wasu ‘yan siyasa irin Umar Maggi Gama, Nura Dankadai da irinsu Muhuyi Rimingado, Farfesa Dahiru Shu’aibu da Farfesa Auwal Arzai.

Daga bangaren mata, an samu Aisha Kaita, Sadiya Abdu Bichi da kuma Aisha Lawan Saji.

Nadin Sunusi Bature Dawakin-Tofa

A jiya aka samu labari cewa Sunusi Bature Dawakin-Tofa ya zama Sakataren yada labarai na zababben Gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf a Jihar Kano.

Kafin yanzu, Malam Bature Dawakin-Tofa ya yi aiki da FCDO, USAID, Melinda Gates da Rockefeller. Shi din kwararren ‘dan jarida ne da ya rike mukamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel