“Ku Kwamushe Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi”: IPAC Ga DSS

“Ku Kwamushe Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi”: IPAC Ga DSS

  • Kungiyar nan ta inganta zumunta a tsakanin jam'iyyun siyasa wato IPAC ta aika muhimmin sako ga hukumar DSS
  • IPAC ta bukaci rundunar tsaro ta farin kaya da su kwamushe wadanda ke kulla-kullan kafa gwamnatin wucin gadi
  • Ta ce masu kitsa wannan shiri suna son kawo tangarda ga tsarin damokradiyya don haka babban abun da ya dace shine a hukunta su

Shugaban kungiyar inganta zumunta a tsakanin jam'iyyun siyasa wato IPAC, Alhaji Yabagi Sani, ya bukaci rundunar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama wadanda ta yi ikirarin suna shirin kafa gwamnatin wucin gadi.

Sani ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da Channels TV a shirin Politis Today.

Jami'an DSS rike da bindigogi
“Ku Kwamushe Masu Yunkurin Kafa Gwamnatin Wucin Gadi”: IPAC Ga DSS Hoto: Sahara Reporters
Asali: UGC

A ranar Laraba ne hukumar DSS ta bayyana cewa wasu yan siyasa na kulla-kulla don kafa gwamnatin wucin gadi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata Uwa Ta Koka Bayan Karamin Danta Ya Zubar Da Madarar N16k a Kasa, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Rundunar tsaron ta kara da cewar yan siyasan sun samo umurnin kotu da zai kawo cikas ga rantsar da sabbin gwamnatoci da majalisu a matakin jiha da kasa, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar DSS zai ci gaba da ta da hankali da haifar da rikici, IPAC

Sai dai da ake hira da shi Sani ya ce:

"Idan su (DSS) sun san wannan mutumin da ke yi wani abu da ya saba damokradiyya don kawo karan tsaye ga tsarin, ina ganin abu mafi dacewa ko abun da ya kamata ayi bisa doka shine tsare mutumin da yi masa tambayoyi.
"Sannan ne sai su iya fitowa su ce an kama wane da laifi. Amma furta wannan zai ci gaba da haifar da tashin hankali da rikici ne kamar bamu da katabus."

APC da PDP sun yi martani kan batun shirin kafa gwamnatin wucin gadi

Kara karanta wannan

Gwamnatin wucin gadi: PDP da APC sun ba DSS shawarin wasu 'yan siyasa a Najeriya

A wani lamari makamancin wannan, kwamitocin yakin neman zaben shugaban kasa jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) sun kalubalanci hukumar DSS a kan gargadin wasu yan siyasa da ta yi.

Jam’iyyun sun bukaci rundunar tsaron ta farin kaya da ta dauki tsatsauran mataki kan masu shirin kafa gwamnatin wucin gadi.

Sun ce yunkurin kafa gwamnatin wucin gadi ya saba ma kundin tsarin mulkin kasar don haka dole a kama masu shirya munakisan tare da bayyana sunayensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel