Matan Sun Fito Zanga-Zangar Adawa da Nasarar Sabon Gwamnan Kaduna

Matan Sun Fito Zanga-Zangar Adawa da Nasarar Sabon Gwamnan Kaduna

  • Daruruwan mata sun gudanar da zanga-zanga domin nuna adawarsu da abinda suka kira fashin kujerar gwamna
  • Jagororin tafiyar, Honorabul Maria Dogo da Hajiya Aisha Ibrahim Madina sun ce ba zasu yarda ba, PDP ce ta lashe zaɓen gwamna a Kaduna
  • Sun nemi hukumar zaɓe ta sake tunani kuma ta fito fili ta ayyana Isah Ashiru a matsayin halastaccen sabon gwamna

Kaduna - Dandazon mata sanye da bakaken kaya na jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) yanzu haka sun fantsama zanga-zanga a cikin garin Kaduna.

Leadership ta tattaro cewa matan sun tsunduma zanga-zanga ne domin nuna adawa da ayyana Uba Sani na jam'iyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Kaduna.

Zanga-zanga a Kaduna.
Matan Sun Fito Zanga-Zangar Adawa da Nasarar Sabon Gwamnan Kaduna Hoto: PDP
Asali: Facebook

Bayan kammala tattara sakamako, INEC ta ce Uba Sani ne zaɓaɓɓen gwamna bayan samun kuri'u mafiya rinjaye a zaben ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An kama wasu da ke sace yara da sunan za su kaisu gidan marayu a jihar Arewa

Jagororin matan da suka hita zanga-zangar, Honorabul Maria Dogo da kuma Hajiya Aisha Ibrahim Madina, sun ce an yi wa jam'iyyarsu fashin cin zaɓe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabannin matan sun yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta sake nazari kan sakamakon kuma ta ayyana Isah Ashiru Kudan na PDP a matsayin halastaccen wanda ya samu nasara.

Matan sun ayyana sakamakon zaben da INEC ta bayyana da fashi da tsakar rana ido na ganin ido, wanda ba za su aminta da shi, zasu kalubalance shi kamar yadda doka ta tanada.

Sun ƙara da jaddada cewa mazauna Kaduna daga lungu da sako sun yi magana da murya ɗaya lokacin zabe wanda ya nuna sun aminta da jam'iyyar PDP.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa matana sun gudanar da zanga-zangar ne a babbar Sakatariyar ƙungiyar 'yan jarida (NUJ) reshen Kaduna.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Jihar Enugu Mai Cike da Ruɗani

Majalisar Dokokin Jihar Ƙogi Ta Dakatar Yan Majalisu 9

A wani labarin kuma Rigima Ta Ɓalle, Majalisa Ta Dakatar da 'Yan Majalisu 9 da Ciyamomi 8 a Jihar Kogi

Majalisar ta fara muhawara ne bayan kakaki ya karanta wasikar gwamna Yahaya Bello, wanda ya sanar cewa ana zargin 'yan majalisun da hannu a aikata ta'addanci.

Bayan haka majalisar ta kuma dakatar da shugabannin kananan hukumomi 8 bisa tuhuma guda biyu bayan samun rahoto daga Kansiloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel