Bola Tinubu Ya Bada Sunayen Wasu Mutum 2 a Kwamitin Karbar Shugabancin Najeriya

Bola Tinubu Ya Bada Sunayen Wasu Mutum 2 a Kwamitin Karbar Shugabancin Najeriya

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kawo mutanen da za su wakilce shi a cikin kwamitin PTC
  • SGF ya ce zababben shugaban na Najeriya ya bada sunayen Atiku Bagudu da Olawale Edun
  • Tsohon Kwamishinan kudin da Gwamnan jihar Kebbi za su yi aiki da sauran ‘yan kwamitin

Abuja - Zababben shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kawo sunayen mutane biyu da za su shiga cikin kwamitin karbar mulki na PTC.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya cike gurbin da Muhammadu Buhari ya ba shi a cikin kwamitin PTC da aka kafa.

A ranar Talata, Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban PTC na kasa, Mista Boss Mustapha, ya ce an sa Sanata Atiku Bagudu da Cif Olawale Edun.

Atiku Abubakar Bagudu shi ne Gwamnan jihar Kebbi kuma shugaban gwamnonin APC yayin da Olawale Edun ya taba yin Kwamishinan kudi a Legas.

Kara karanta wannan

Toh fa: Sanata ya ba da shawarin a ba Buhari wata babbar kujera a Najeriya bayan mika mulki

An shigar da Bagudu da Edun

Sanata Atiku Abubakar Bagudu yana cikin Gwamnoni masu shirin barin mulki a Mayun 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Boss Mustapha ya ce kwamitin karbar mulkin ya soma aiki da nufin ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya mika mulkin kasar salin alin ga Bola Tinubu.

Bola Tinubu
Bola Tinubu cikin masoya Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

PTC ya yi zama hudu a Abuja

SGF din ya shaidawa manema labarai ce tun bayan da Mai girma Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin PTC, sun yi zama sau hudu kenan zuwa yanzu.

"Bayan an sanar da wanda ya ci zabe, PTC ya bukaci Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa mai jiran gado ya kawo sunayen mutane biyu.
Zababben shugaban kasar ya bada Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Olawale Edun."

- Boss Mustapha

Jaridar ta ce sauran ‘yan kwamitin da ke karkashin SGF sun hada da kananun kwamitin yada labarai, harkar addini, zirga-zirga, fareti da dai sauransu.

Kara karanta wannan

"Dama Na Faɗa" Gwamna Wike Ya Maida Martanin Kan Maye Gurbin Shugaban PDP Na Kasa

Aikin kwamitin nan ya hada da tsara laccocin mika mulki, liyafa, bukukuwan yara, aika goron gayyata, sufuri, rantsarwa, kula da lafiya da makamantansu.

Zanga-zanga a kan zaben 2023

Kusan tinbir aka samu labari wasu fusatattun mata suka yi zanga-zanga a Birnin Abuja domin ankarar da Gwamnaitin Amurka a kan zaben shekarar nan.

Yayin da matan suke zanga-zanga a watan Azumi, magoya bayan Bola Tinubu sun yi na su tattakin saboda su nunawa Duniya su na tare da zababben shugaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel