Mata Sun Yi Zanga-Zanga Zindir Kan Zaben Najeriya a Ofishin Jakadancin Amurka a Ramadan

Mata Sun Yi Zanga-Zanga Zindir Kan Zaben Najeriya a Ofishin Jakadancin Amurka a Ramadan

  • An samu fusatattun matan da suka shirya zanga-zanga a ofishin Jakadancin kasar Amurka
  • Matan da ke cikin kungiyar Free Nigeria Movement ba su ji dadin abin da ya faru a zaben 2023 ba
  • Domin nuna matsayar da suka dauka, wadannan Bayin Allah sun yi zanga-zangar ne babu tufafi

Abuja - A ranar Litinin, wasu fusatattun mata su ka yi zanga-zanga a gaban ofishin Jakadancin kasar Amurka a Najeriya da yake birnin Abuja.

Vanguard da ta dauko wannan rahoto ta ce masu zanga-zangar sun cire wasu daga cikin kayan jikinsu domin nuna rashin jin dadin zaben 2023.

Matan na kungiyar Free Nigeria Movement sun je ofishin Jakadancin ne da nufin kokawa Duniya abin da suke cewa magudi da aka yi a zaben bana.

Masu zanga-zangar sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin Amurka ta hukunta wadanda suke da hannu wajen tada rikici wajen neman takara.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Ana so Amurka ta dauki mataki

Rahoton yake cewa matan su na so kasar Amurka ta hana masu wannan aika-aika takardar biza.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadannan Bayin Allah da suka shirya zanga-zanga a farkon makon nan, ba su kama sunan wani ‘dan siyasa bisa zargin ya na da laifin magudi ba.

Amurka
Ofishin Jakadancin Amurka Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Mata sun cire rigunansu

Saboda su nuna fushinsu a zahiri, wadannan mata da ke neman ayi gaskiya su ka cire wasu kayan jikinsu yayin da ake tsakiyar watan azumi a Duniya.

Linda Ikeji ta ce makasudin zanga-zangan shi ne a hukunta wadanda suka kawo tarnaki a zaben Gwamnonin jihohi da na shugaban kasa da majalisa.

A daidai lokacin da ake wannan zanga-zanga, sai aka samu wasu gungu na dabam a garin na Abuja su na tattaki domin nuna goyon baya ga Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Sahara Reporters ta ce masoyan na Bola Tinubu sun yi zanga-zangar su ne domin nuna ba su goyon bayan a kafa gwamnatin rikon kwarya a Najeriya.

Tun da hukumar INEC ta ayyana jam’iyyar APC a matsayin wanda ta lashe zaben shugaban kasa, ake samun ra’ayi masu cin karo da juna a kasar nan.

Bayo Onanuga ya ga ta ka shi

Kafin nan labari ya zo cewa wani Farfesa ya kai batun Darektan yada labarai a kwamitin yakin zaben Bola Tinubu, Bayo Onanuga zuwa ICC a Hague.

Babban kotun ICC na Duniya ya karbi wannan korafi mai lamba OTP-CR-109/23 a ranar Litinin dinnan kamar yadda Mark P. Dillon ya sa hannu a takardar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel