Rikicin PDP ai Yanzu Aka Fara – Fitaccen Gwamna Ya Ragargaji Shugaban Jam’iyya

Rikicin PDP ai Yanzu Aka Fara – Fitaccen Gwamna Ya Ragargaji Shugaban Jam’iyya

  • Gwamnan jihar Ribas bai yarda Dr. Iyorchia Ayu ya cigaba da jagorantar jam’iyyarsu ba
  • Nyesom Wike ya ce ko me za faru, sai da ya faru, amma dole Jam’iyyar PDP tayi sabon shugaba
  • Mai girma Wike ya yi kaca-kaca da Ayu yayin da ya bude wata makaranta a garin Obio-Akpor

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya nuna a rikicin cikin gidan PDP, Shugaban jam’iyya na kasa, Iyorchia Ayu bai ga komai ba tukuna.

A yammacin Litinin, tashar talabijin nan na Channels TV ta rahoto Nyesom Wike yana faadwa Dr. Iyorchia Ayu, rigimar jam’iyyar PDP, yanzu ne aka soma.

Gwamnan na jihar Ribas ya yi wannan magana ne dazu a yayin da yake kaddamar da makarantar sakandaren Okoro-nu-Odo da gwamnatinsa ta gyara.

A bayanin da ya yi a yankinsa na karamar hukumar Obio-Akpor a jihar Ribas, Mai girma Nyesom Wike ya ce babu yadda Dr. Ayu zai cigaba da zama a ofis.

Kara karanta wannan

Abu Ya Girma: Babbar Kotu Ta Dakatar da Shugaban PDP Na Ƙasa Nan Take Kan Muhimmin Abu 1

Wajibi ne a sauke Ayu - Wike

Rahoton da ya zo Daily Trust ya nuna Gwamnan bai gamsu Ayu ya rike kujerar shugaban jam’iyya alhali PDP ta rasa mazaba, kauye da jiharsa a zabe ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tambayi su masu son shugaban jam’iyyar PDP, me zai ba jam’iyyar yanzu? Zaben shugaban kasa; ka rasa rumfarka, mazabarka, karamar hukumarka da jiharka.
Wace jam’iyya za ka jagoranta?

- Nyesom Wike

Wike.
Nyesom Wike da mutanensa Hoto: @GovernorNyesomEzenwoWike
Asali: Facebook

Ina ma Ayu ya yi murabus

Wike yana ganin cewa kunnen kashin Ayu ya hana shi yin murabus lokacin da ‘Yan G5 da ‘yan taware suka bukaci ya sauka daga kujerar da yake kai.

Gwamnan na jihar Ribas yake cewa tun farko da shugaban na PDP ya yi murabus, da zai samu uzurin da zai fake da shi yayin da PDP ta fadi zaben 2023.

Kara karanta wannan

Maganar Tsige Shugaban PDP Tayi Karfi, Rikicin Jam’iyya Ya Cigaba da Jagwalgwalewa

Sun ta rahoto Mai girma Gwamnan yana cewa ganin yadda aka yi wa jam’iyyarsu ta PDP dukan sakwara, bai kamata Ayu ya cigaba da jagorantar NWC ba.

Masu fada saboda an dakatar da shi, ba ku ga komai ba tukuna. Yanzu aka fara fadan.
Ayu, yanzu aka fara fadan. Wadanda su ka sans hi, wadanda suke kusa da shi, ku fadawa Iyorchia Ayu, fada yanzu aka soma.

A karshe Gwamnan ya ce shugabannin PDP za su ga abin da yara za su yi masu, a cewarsa ba za ta yiwu a juya jam’iyya da kudinsu, Ayu yana ofis ba.

Shirin zaben Gwamnoni

Ku na da labari a zaben sabon Gwamnan jihar Kogi da za ayi, Sanata Smart Adeyemi, Sanusi Ohiare da James Faleke sun lale N50m a wajen sayen fam.

Haka zalika za a fafata da Mataimakin Gwamna, Edward Onoja wajen samun tikitin APC domin neman Gwamnan Kogi a zaben da za a shirya a Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Rikici Ya Tsananta, Gwamna Wike Ya Maida Martani Mai Zafi Kan Dakatar da Shugaban PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel