Maganar Tsige Shugaban PDP Tayi Karfi, Rikicin Jam’iyya Ya Cigaba da Jagwalgwalewa

Maganar Tsige Shugaban PDP Tayi Karfi, Rikicin Jam’iyya Ya Cigaba da Jagwalgwalewa

  • A maimakin rikicin jam’iyyar PDP ya lafa, lamarin neman kara rincabewa yake yi a halin yanzu
  • Uwar jam’iyya ta dakatar da wasu jagorori, hakan ya zama tamkar an sake huro wutar rigima
  • An samu wadanda suka dakatar da Shugaban jam’iyya yayin da ake ta musayar zance a PDP

Benue - Rikicin jam’iyyar PDP ya rikida yayin da shugabannin mazabar Igyorov a karamar hukumar Gboko a Benuwai suka dakatar da Iyorchia Ayu.

Daily Trust ta ce hakan yana zuwa ne a lokacin da uwar jam’iyyar PDP ta kasa a karkashin jagorancin Iyorchia Ayu ta dakatar da Gwamna Samuel Ortom.

Majalisar NWC ta dauki irin wannan mataki a kan Ayodele Fayose, Anyim Pius Anyim da wasunsu. A karshe hakan sai da ya kara jagula matsalolin.

Da shugabannin Igyorov suka tashi, sun nuna jam’iyyar PDP a mazabar ba ta gamsu da rikon Iyorchia Ayu ba, ta zarge shi da yi mata zagon kasa a zabe.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Akayi Masa

Ana wata ga wata a PDP

Vangeryina Dooyum a matsayin Sakataren PDP ya fitar da jawabin da mutum 12 daga cikin shugabanni 17 na mazabar Igyorov duk suka rattabawa hannu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana haka kuma sai ga Kakakin jam’iyyar PDP na reshen jihar Benuwai, Bemgba Iortyom, ya fitar da jawabi yana cewa su na tare da Mai girma Samuel Ortom.

Iyorchia Ayu
Iyorchia Ayu da Atiku Abubakar Hoto: www.voiceoflibertyng.com
Asali: UGC

Rahoton ya ce jawabin da aka fitar a Makurdi ya soki matakin da shugabannin PDP na kasa suka dauka a kan Ortom da wasu abokan tafiyarsa a jam’iyya.

Shi ma Gwamna Nyesom Wike ya yi fatali da dakatarwar da ake cewa an yi wa Fayose da wasunsa, ya ce matsayar nan da aka dauka ba za ta zauna ba.

Sabon faifen rikici ya budu

Nyesom Wike ya ce Ayu da mutanensa sun bude sabon babin rikici a jam’iyyar PDP, hakan ya nuna ba a kama hanyar kawo karshen rikicin cikin gidan ba.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: PDP Ta Dakatar Da Shugabanta Na Kasa, Iyorchia Ayu, Ta Fadi Dalili

Kungiyar G5 na Gwamnonin da ke adawa da takarar Atiku Abubakar a 2023 da Nyesom Wike ya jagoranta, ta dage cewa dole sai Ayu ya bar kujerarsa.

Sanata Ayu wanda ya karbi shugabancin jam’iyya ya nuna ba zai sauka ba, yayin da wasu suke ganin labarin zai iya canzawa bayan zaben shugaban kasa.

Ibrahim Shema zai bar PDP?

Rahoto ya zo a baya cewa Ibrahim Shema wanda bai taba barin Jam’iyyar PDP ba, yana maganar sauya-sheka bayan fitar da sanarwa cewa an dakatar da su.

Tsohon Gwamnan wanda yana cikin majalisar NEC da BOT ya ba NWC kwana 2 ta dawo da shugabannin jam'iyya da aka tsige a Katsina, ya ce an saba doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel