Rikicin PDP: Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Akayi Masa

Rikicin PDP: Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Akayi Masa

  • Tun bayan faduwar jam’iyyar PDP a manyan zabukan Najeriya na 2023, PDP ta shiga halin rai-kwakwai-mutu-kwakai
  • Rikicin da ya mamaye jam’iyyar bai bar Shugaban jam’iyyar ba, domin saida aka dakatar dashi daga mazabar sa
  • Sai dai ta bakin kakakin shugaban jam’iyyar PDP, Imobo –Tswam yace Ayu bai dakatu ba, saboda wasu hujjoji daya zayyana

Abuja - Rikicin jamiyyar PDP na kara canja salo tun bayan faduwa da jam’iyyar tayi a manyan zabukan kasa na 2023 daya wuce.

A cikin turka-turkan dake ci gaba da faruwa. Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu yayi fatali da dakatarwar da wani tsagi na masu fada aji a mazabar sa suka bayar.

Sudai wadannan tsagin na masu fada aji, suna zargin Ayu ne akan yin ayyuka dake nuna yana yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Rikicin PDP
Rikicin PDP: Shugaban Jam’iyyar PDP Ayu Yayi Fatali da Dakatarwar da Akayi Masa Hoto: Vanguard.ng Asali: UGC
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daga nashi bangaren, Ayu ya alakanta wannan dakatarwar a matsayin aikin wasu yan gaba-gadi masu gaggawa da mafarkin ganin sun fada aji ta kowanni hali. Inda ya kirasu da yan cacan da basu san meye kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ba.

Ayu ya bayyana haka ne a wani bayani daya sawa hannu ta wajen mai magana da yawun sa, Simon Imobo -Tswam a ranar Litinin din nan a Abuja.

Mai Magana da yawun na Ayu yace, anja hankalin shugaban na PDP akan dakatarwar maras ka’ida, saboda haka ya bada martani da cewar:

“Mazabar Shugaban jam’iyyar PDP Dr. Iyorchia Ayu bata dakatar dashi ba. Wadanda sukai wannan aikin sun samu tilastawa da umarni ne daga ‘yan cacan siyasa, domin su tada zaune tsaye kawai.

Ya kara da fadin

Kara karanta wannan

Za ku sha mamaki: Sabon gwamnan wata jiha ya fadi yadda zai ji da albashin ma'aikata a jihar

“Ga yan koyon ilimin siyasa, Sashi na 57 (7) na kundin tsarin mulkin PDP wanda aka gyara a 2017 ya haramtawa wani bangare ko kwamiti dake jam’iyya a matakin mazaba, ko jiha akan daukan matakin ladabtarwa ga wani da yake jagora ne a matakin kasa”.

Ya nausa cikin bayanin sa da cewa:

“Dakatarwar a nan, ba zata haifar da diya mai ido ba, saboda ta samo asali ne daga rashin ilimi, yan cacan siyasa da son mulki da iko. Kuma ba komai bane face dirama da kuma farfaganda”.

Bayanin ya nuna yadda aka saci sanya hannun wadanda ake zargin sun sanya hannu domin a dakatar da shugaban na PDP ta hanyar yin amfani da karfi tare da boye su.

Jaridar Vanguard ta ruwaito yadda Simon Imobo -Tswam ya zargi masu kitsa laifin da kashe wayoyin Excos din wanda hakan ke nuni da sanya su akai ta karfi ba yin kansu bane.

Kara karanta wannan

“Karku Rantsar da Tinubu Domin Yin Hakan Ya Sabawa Dokar Tsarin Mulkin Najeriya” - Baba Ahmed

Daga karshe kakakin Ayu ya nemi mutane da suyi watsi gamida fatali da dakatarwar.

An Dakatar da Ayu Bisa Zargin Yin “Anti Fati”

Rikicin jam’iyyar PDP na cigaba da kara ta’azzara yayin da wasu gungun masu fada aji suka dakatar da shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dr Iyorchia Ayu.

Masu fada ajin na jam’iyyar da suka fito daga gudunmar Igyorov dake can karamar hukumar mulki ta Gboko sunce matakin dakatarwar ya zama dole, kuma dakatarwar tanan take ce.

Masu dakatarwar na zargin Ayu ne akan zargin tadiye jam’iyyar tare da yi mata mamakon zagon kasa maras misaltuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mustapha Abubakar avatar

Mustapha Abubakar

Online view pixel