Peter Obi Ya Tona Komai, Ya Fadi Wasu Jihohi 2 da Jam'iyyar APC Ta Murde Masa Kuri’u

Peter Obi Ya Tona Komai, Ya Fadi Wasu Jihohi 2 da Jam'iyyar APC Ta Murde Masa Kuri’u

  • Peter Obi ya na da’awar cewa jam’iyyarsa ta LP ce ta yi nasara a zaben 2023, amma aka murde
  • ‘Dan takaran shugaban kasar yana so a soke wasu kuri’un a INEC ta ba Bola Tinubu da APC
  • Jam’iyyar LP ta je kotun sauraron karar zabe, ta na so a sake shirya zaben shugaban Najeriya

Abuja - Peter Obi da jam’iyyarsa ta LP sun roki kotu ta dawo masu da kuri’un da suke ikirarin sun samu a zaben sabon shugaban kasa da aka yi.

Premium Times ta kawo rahoto cewa Peter Obi yana so a soke zaben wannan shekarar, a kuma shirya wani sabon zaben na shugaban Najeriya.

‘Dan takaran na jam’iyyar adawa ta LP ya bukaci kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa a Abuja ya soke kuri’un da aka ba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku: Yadda Aka Yi Amfani da Wata Na’ura, Aka Zaftare Mani Kuri’u a Zaben 2023

Ana sa ran nan da wani lokaci, Lauyoyin Hukumar INEC, jam’iyyar APC, Bola Tinubu da Kashim Shettima za su maidawa Lauyoyin LP martani.

Peter Obi
Peter Obi da Datti Baba Ahmed Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyoyin da suka shigar da kara a Abuja sun roki kotun korafin zabe ta dawo masu da kuri’un da take cewa an murde masu saboda APC ta ci zabe.

Jam’iyyar LP ta na ikirarin ita tayi nasara a zaben shugaban kasa a Ribas, amma a karshe hukumar INEC ta ce APC ta fi kowa kuri’u a jihar Kudun.

Kuri'un da aka murde a Benuwai da Ribas

Haka zalika Obi ya yi ikirarin jam’iyyar LP ta fi kowa yawan kuri’un da aka kada a Benuwai, amma a nan ma aka ce Bola Tinubu ne ya yi galaba.

Takardun karar sun nuna LP ta fadawa kotu mutane 205,110 suka zabi Obi a Ribas, sai mutum 84,108 su ka kada kuri’arsu ga APC, ratar 121,002 kenan.

Kara karanta wannan

Shekarau da Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara 10 da 20 a Zaben Bana

A Benuwai kuwa, masu karar su na cewa gaskiyar abin da ya faru a zaben shugaban kasa shi ne LP ta na da kuri’u 329,003, sai APC ta samu 300,421.

Za a buga a kotun zabe

Haka zalika a karar da yake yi a gaban kotu, Peter Obi ya ce tun da an taba samun Bola Tinubu da aikata laifi a kasar Amurka, bai dace da takara ba.

Lauyoyin da LP ta dauka sun fake da sashe na 137 na kundin tsarin mulki, su ka ce doka ba ta yarda a nada wanda kotu ta taba samu da laifi ba.

Atiku ya kai karar APC da INEC

A gefe, an samu labari Lauyoyin Atiku Abubakar sun gabatar da hujjoji a kotun da ke sauraron karar zabe, sun ce Bola Tinubu bai lashe zabe ba.

Joe Kyai Gadzama SAN ya roki kotun karar zabe ta ce Atiku ne zababben shugaban Najeriya a maimakon Bola Tinubu da INEC ta ba satifiket.

Kara karanta wannan

Ana Neman Hana Tinubu Hawa Mulki, Atiku Ya Kinkimi Lauyoyi, An Garzaya Kotun Zabe

Asali: Legit.ng

Online view pixel