Zaben 2023: Gwamna Umahi Ya Baiwa Atiku Abubakar da Peter Obi Shawara

Zaben 2023: Gwamna Umahi Ya Baiwa Atiku Abubakar da Peter Obi Shawara

  • Gwamnan jihar Ebonyi ya sake taya shugaban kasa mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima murnar nasarar da Allah ya basu
  • David Umahi ya roki manyan yan takarar shugaban kasa biyu da suka garzaya Kotu da su canza shawara
  • Ya bukaci Peter Obi da Atiku Abubakar su janye kara su runguma kaddarar Allah kuma su zo a ci da ƙasar nan gaba

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya roki, Peter Obi, Atiku Abubakar da sauran waɗanda suka fafata a zaben shugaban ƙasa su rungumi kaddara kana su zo a haɗa hannu wajen gina Najeriya.

Umahi ya yi wannan roko ne a wani shirin kai tsaye da taron manema labarai wanda ya gudana ranar Laraba a gidan gwamnatinsa da ke Abakaliki.

Atiku Abubakar da Peter Obi.
Manyan 'yan takara 2, Atiku da Peter Obi Hoto: Atiku & Obi
Asali: Facebook

Umahi ya buƙaci 'yan takarar su ɗauki nasarar Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin haka Allah ya tsara kuma su kaucewa batun shigar da ƙara, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shin Dagaske Neman Lafiya Ya Tafi? Tinubu Ya Shilla Kasar Waje, An Fallasa Abubuwan Ya Zai Yi

Ya kuma yaba wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da Ciyaman ɗin INEC ta kasa, Farfesa Mahmud Yakubu, bisa sabbin ci gaban da suka kawo a bangaren zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, waɗannan sabbin abubuwan da suka kirkiro zai ci gaba da inganta matakan gudanar da zaɓe a Najeriya. Ya kara da cewa ya kamata burin kowane shugaban siyasa ya karkata kan gina ƙasa.

"Bari na ƙara taya zabaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu, murna tare da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, bisa nasarar da Allah ya basu."
"Ina rokon ɗan uwanmu, mai girma Peter Obi, da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, su amince da hukuncin Allah, su zo a haɗa hannu wajen gina sabuwar Najeriya."

Daga nan, gwamna Umahi ya yaba wa mutanen jihar Ebonyi bisa nuna masu ana tare suka zabi jam'iyyar APC a zaben gwamnan da aka kammala, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Taya Tinubu Murna Bayan Kwana 21, Ya Nemi Bukata 1 a Gwamnatinsa

Abinda Ya Sa Bola Tinubu Ya Fita Najeriya Zuwa Kasar Waje, Tunde

A wani labarin kuma Hadimin Bola Tinubu ya bayyana abinda uban gidansa ya tafi yi ƙasar waje

Tunde Rahman, ya ce shugaban kasa mai jiran gado ya tafi hutu Faransa, daga can zai wuce ya yi aikin Umrah a kasa mai tsarki lokacin Azumin Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel