Shugaba Buhari Da Sunayen Mutum 7 da Yake Son Naɗa Wa a NDIC

Shugaba Buhari Da Sunayen Mutum 7 da Yake Son Naɗa Wa a NDIC

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sunayen mutane 7 ga majalisar Dattawa domin ta tantance su glya naɗa su a NDIC
  • Shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya karanta wasiƙar bukatar shugaban kasan a zaman yau Talata
  • Ya karanta sunayen mutanen da Buhari ya nemi naɗa wa a majalisar gudanarwa ta hukumar NDIC daga shiyyoyin kasar nan

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya roki majalisar dattawa ta tantance tare da sahale masa naɗin mutane 7 a hukumar Inshora ta ƙasa (NDIC), kamar yadda The Nation ta rahoto.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ne ya karanta wasikar da shugaba Muhammadu Buhari da aiko da bukatar a zaman majalisa na ranar Talata.

Shugaban kasa Buhari
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a Aso Villa Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Waɗanda shugaban kasan ya naɗa a cewar Lawan, sun kunshi Dakta Abdulhakeem Mobolaji, daga kudu maso yamma a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na NDIC.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Yi Sabon Nadi Mai Muhimmanci Ana Daf Da Karewar Wa'adinsa A Watan Mayu

Sauran sun haɗa da Farfesa Osita Okwu (mamba) daga shiyyar kudu maso gabas, Uwa Gambo Jubril a matsayin mamba daga arewa ta tsakiya da Mohammed Attahiru Haruna a matsayin mamba daga arewa maso gabas.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sauran mambobin su ne, Yesmil Dalhatu, daga shiyyar arewa maso yamma, Simon Ovie, daga shiyyar kudu maso kudu da kuma Abimbola Olasore, wanda zai wakilci shiyyar kudu maso yamma.

A rahoton Punch, wani sashin wasikar Buhari ya ce:

"Bisa la'akari da tanadin sashi na 5 (4) a kundin dokokin hukumar inshora, na turo wa majalisa waɗan nan sunayen domin tabbatar da su a matsayin mambobin majalisar gudanarwa ta hukumar NDIC."
"Takardan da ta ƙunshi bayanansu na haɗe da wannan wasikar, ina fatan majalisa zata yi kyakkyawan duba kan wannan abu da na gabatar."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Lokaci Ya Yi Da Nima Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Kalu Ya Magantu

Wannan naɗin da Buhari ya yi na zuwa yayin da ya rage watanni 2 da 'yan kwanaki wa'adin mulkinsa ya ƙare a rantsar da sabon shugaban kasan da yan Najeriya suka zaɓa.

Emefiele ya nemi afuwar yan Najeriya

A wani labarin kuma Gwamnan CBN Ya Baiwa Yan Najeriya Hakuri Kan Matsalar da suka sha fama da ita wajen tura kuɗi ta asusu

Mista Godwin Emefiele, yace abubuwa ne suka sha musu kai a lokacin amma yanzun an warware komai.

Ya kuma gargaɗi masu hannu jari da bankuna su kwana da shirin cewa gwamnati zata ita soke lasisin da ta basu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel