Lokaci Ya Yi Da Nima Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Kalu Ya Magantu

Lokaci Ya Yi Da Nima Zan Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Kalu Ya Magantu

  • Zababben sanatan Abia North, Orji Kalu, ya ce lokaci ya yi da zai sama shugaban majalisar dattawa a yayin da ake shirin yin sabon zubi
  • Kalu ya ce lokacinsa ya yi na zama shugaban majalisa na gaba kuma ya yi kira ga jam'iyyar na APC ta mika shugabancin majalisar zuwa kauyensa ta Igbere a Abia North
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata da safe yayin zantawa da manema labarai a majalisar tarayya

FCT, Abuja - Bulaliyar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, ya sanar da niyyarsa na yin takarar shugabancin majalisar tarrayya zubi na 10.

Kalu, wanda ya yi tararce don cigaba da wakiltar Abia North a majalisar dattawan, ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya ke jawabi ga manema labarai a majalisar tarayya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ta Kwace Mulki Daga PDP, Babban Malami Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Arewa

Orji Kalu
Yanzu Lokaci Na Ne Na Zama Shugaban Majalisar Dattawa, Kalu Ya Magantu. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar ta All Progressives Congress mai mulki a kasa ita ke da rinjaye a majalisar, inda ta samu kujeru 57.

Sanatocin APC da ke kwadayin dare wa kujerar shugabancin majalisar sun fara bibiyan takwararinsu don neman goyon bayansu.

Baya ga Kalu, wanda ya sanar da niyyarsa a fili, Godswill Akpabio (Akwa Ibom); Sani Musa (Niger); Barau Jibrin (Kano); da Dave Umahi (Ebonyi) suma sun nuna sha'awarsu na darewa kan kujerar.

A karshe dai za a zabi wanda zai dare kujerar ne ta hanyar kada kuri'a.

Kawo yanzu jam'iyyar ta APC ba ta ware kujerar shugabancin majalisar zuwa kowanne bangare ba.

Kalu ya bayyana dalilin da yada ya kamata ya zama shugaban majalisa na gaba

A bidiyon da Daily Trust ta wallafa a Twitter, tsohon gwamnan na jihar Abia ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke zantawa da yan jarida a majalisar tarayya a ranar Talata, 21 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Zababben sanatan ya kuma yi kira ga jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta mika shugabancin majalisa na 10 ga kauyensa na Igbere da ke mazabar Abia North.

A cewarsa, idan aka yi la'akari da matsayinsa na babban bulaliyar majalisa na 9, shine sanata mafi mukami mai girma daga kudu maso gabas, don haka, ya cancanci mukamin.

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan da APC, Orji Kalu, Shugabancin Majalisa, Zaben 2023, Kudu maso Gabas

Ya ce sunansa na farko da tsakiya da karshe duk zai zama tawagar Najeriya, ya kara da cewa shi kadai ne gwamnan da bai taba canja lambar wayarsa ba tun kimanin shekaru 24 da ya zama gwamna.

Ya ce yana da niyyar cigaba da amfani da lambar don amsa kiran mutane.

Ya ce:

"Ba zan kashe waya ta ba domin nine shugaban majalisa na gaba, a'a, amma ina fatan yan Najeriya za su min addu'a in zama shugaban majalisa don lokaci na ne."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: PDP ta yi jana'izar APC, ta lashe kujerar majalisa ta farko a jihar APC a Arewa

Ga bidiyon:

PDP ta ce za ta tafi kotu game da sakamakon zaben gwamnan Katsina

A bangare guda, jam'iyyar PDP, a jihar Katsina ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Mustapha Inuwa, shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku/Lado ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel