Siyasa Babu Gaba: ‘Dan takara ya Taya Abba Kabir Yusuf Murnar Karbe Gwamnati a Kano

Siyasa Babu Gaba: ‘Dan takara ya Taya Abba Kabir Yusuf Murnar Karbe Gwamnati a Kano

  • Sha’aban Ibrahim Sharada bai dauki siyasa da gaba ba, ya taya Jam’iyyar NNPP samun nasara
  • ‘Dan takaran ya roki Allah (SWT) ya yi riko da hannuwan Abba Kabir Yusuf da zai karbi mulki
  • Hon. Sharada ya jinjinawa aikin Hukumar zabe, yake cewa sun yi wa Kanawa abin da ya dace

Kano - Sha’aban Ibrahim Sharada yana cikin wadanda suka nemi takarar Gwamna a jihar Kano, amma bai samu nasara ba.

Bisa dukkan alamu, Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya rungumi kaddara kamar yadda maganganunsa a Twitter suka nuna.

‘Dan majalisar wakilan tarayyan ya taya murna ga Injiniya Abba Kabiru Yusuf, ya kuma nuna Hukumar zabe ta INEC ta yi daidai.

Honarabul Sharada ya yi addu’a ga zababben gwamnan, ya daura wasu hotunansa tare da shi.

Sha'aban ya taya Abba, Kwankwaso murna

Kara karanta wannan

Abba Gida-gida: Sabon gwamnan Kano ya yi magana, ya fadi abin da ya shiryawa Kanawa

Kamar yadda za a gani a bayanin ‘dan takaran gwamnan na jam’iyyar ADC mai alamar littafi, an ga hotonsa tare da Rabiu Kwankwaso.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sha'aban Sharada
Sha'aban Sharada da Abba Gida Gida Hoto: @Shaabansharada
Asali: Twitter

“Alhamdulillah Ma sha Allah, lallai Allah Mai Girma ne. Hukumar INEC tayi wa mutanen jihar Kano abin da ya kamata.
Ina taya @Kyusufabba,@KwankwasoRM murna. Ubangiji Allah yayi riko da hannayensa, Amin.

- Sha’aban Ibrahim Sharada

Sharada ya so ya nemi takara a karkashin jam’iyyar APC mai-mulki, da bai dace ba, sai ya yi tsalle zuwa ADP mai alamar littafi.

A zaben sabon Gwamnan da aka yi, matashin yana bayan Abba Kabir Yusuf, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da Muhammad Abacha.

'Yan takaran ADP da PRP sun taya murna

Da wannan, ya zama ‘dan takara na biyu da muka samu labarin ya taya zababben gwamna wanda aka fi sani da Gida-Gida murna.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

Kafin shi, an ji Salihu Yakasai ta bakin Hadiminsa ya fitar da jawabi yana mai taya Abba murna, yace yana sa ran zai kawo cigaba.

Yakasai ya hango faduwa

A baya rahoto ya zo cewa Salihu Tanko Yakasai ya godewa jama'a da ya fahimci lallai babu inda zai je a takarar Gwamnan 2023.

An fahimci cewa Jam’iyyar LP da ba ta da ‘Dan takarar Gwamna a zaben jihar Kano, ta ci kuri’u masu yawa a zaben na Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel