Tsohon Gwamnan PDP Ya Kwankwadi Giya Saboda Murnar Tambuwal Ya Kunyata a Sokoto

Tsohon Gwamnan PDP Ya Kwankwadi Giya Saboda Murnar Tambuwal Ya Kunyata a Sokoto

  • Ayodele Fayose ya yi farin ciki da abin da ya faru da Jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Sokoto
  • Tsohon Gwamnan na Ekiti ‘Dan PDP ne amma yana murna an tika ‘Dan takaran Tambuwal da kasa
  • Fayose ya zargi Gwamnan na Sokoto da cin amanar wadanda suka taimaka masa a tafiyar siyasa

Ekiti – Tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda dadin cewa jam’iyyar PDP za ta bar mulki a jihar Sokoto.

A wani bidiyo da muka ci karo da shi a shafin The Nation a Twitter, an ga Ayodele Fayose ya na murna a kan nasarar APC a zaben Gwamna a Sokoto.

Duk da babu abin da ya hada ‘dan siyasar na Ekiti da Birnin Shehu, ya ce zaben 2023 ya zama sakayya na irin cin amanar Aminu Waziri Tambuwal.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

Fayose ya zargi Aminu Tambuwal da cin amanar jam’iyyar PDP da Bola Tinubu da kuma Gwamna Nyesom Wike da suka taimaka masa a siyasa.

A bidiyon, an ji jigon na PDP yana yabawa al’ummar Sokoto da suka ki zaben Sa’idu Ubandoma, su ka ba Ahmad Aliyu na APC kuri’unsu a zaben bana.

Maganar da Ayo Fayose ya yi

"Jama’a sunana Ayo Fayose, kun san ni kuma na san ku. Ina farin ciki sosai a kan nasarar jam’iyyar PDP a daren yau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga abokai na da suke jam’iyyar APC da suka lashe zabukansu, ina taya ku murna. Ina maku fatan alheri a kujerarku.
Amma bari in yi gaggawar cewa ina mai matukar murna da faduwar ‘dan takaran Gwamna Tambuwal a Sokoto.
Idan mutum maci amana ne, akwai ranar kin dillaci. Ya ci amanar jam’iyya a 2015, ya sauya-sheka.

Kara karanta wannan

Sa’o’i Kadan da Kammala Zabe, Sanata Ya Fice Daga PDP, Ya Rungumi Tinubu da Kyau

Ya ci amanar Asiwaju da ya hadu da shi a APC, sannan ya ci amanar Wike da ya mara masa baya a zaben 2019.

- Ayo Fayose

Kiran karshe ga Sakkatawa

Daily Post ta ce Fayose yana magana yana kwankwadar giya ya yi kira ga mutanen Sokoto su sake kunyata Tambuwal a zaben Sanatoci da za a karasa.

A karshe an ji fitaccen ‘dan siyasar yana cewa Gwamna Aminu Tambuwal ya tafi kenan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel