Zaben Gwamna: Hukumar INEC Ta Sanar da ‘Inconclusive’ a Kebbi

Zaben Gwamna: Hukumar INEC Ta Sanar da ‘Inconclusive’ a Kebbi

  • Hukumar INEC ba ta iya ayyana wanda ya yi nasara a zaben Gwamnan 2023 a jihar Kebbi ba
  • Jam’iyyar APC mai-ci ta na kan gaba a takarar, amma an soke kuri’u daga kusan ko ina a Kebbi
  • Ratar 40000 ba za ta bada damar a ba APC nasara ba domin akwai kuri’u 91000 da aka kashe

Kebbi - A jihar Kebbi, hukumar zabe na kasa watau INEC ba ta iya tsaida wanda ya lashe zaben Gwamna ba, sai an kai ga sake yin wani zagayen.

Daily Trust ta kawo rahoto a daren Litinin cewa wankin hula ya kai dare a zaben sabon Gwamnan Kebbi inda ake fafatawa tsakanin APC da PDP.

A zaben da aka yi a Kebbi, an samu wuraren da aka kada kuri’un da suka yi yawa a kananan hukumomi 20 a cikin kananan hukumomi 21 a jihar.

Kara karanta wannan

APC Ta San Makomar ta, An Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna a Nasarawa

Malamin tattara zaben Gwamna a Jihar Kebbi, Farfesa Yusuf Sa’idu ya ce jam’iyyar APC ta na da 388,258 sai PDP ta samu kuri’u 342,980 a zaben.

An soke kuri'u masu yawa

Jaridar ta ce duk da ratar kuri’u 45,278 da aka samu tsakanin ‘yan takaran, an ki karbar kuri’u 18,204, sannan an soke kuri’un da sun kusa kai 100, 000.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Yayin da ake tattara sakamako, an soke adadin kuri’u 91, 829 a kananan hukumomi 20 a cikin 21.
'Yan APC
'Yan APC na kamfe a Kebbi Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC
"Bisa karfin ikon da nake da shi a matsayin babban malamin tattara zabe kuma jami’in kula da zaben Gwamna, ni Farfesa Yusuf Sa’idu na jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto, na bayyana zaben nan a matsayin wanda bai kammalu ba.

- Farfesa Yusuf Sa’idu

Zaben Gwamnan Kano

A gefe guda, mutane sun kwallafa rai domin jin yadda za ta kaya a Kano, har zuwa yanzu dai hukumar INEC ba ta kai ga fadan sakamakon karshe ba.

Kara karanta wannan

2023: Yadda Ta Kaya da Manyan Masu Neman Takara a Akwatinsu a Zaben Jihohi

Ma’aikatan INEC sun nemi karin lokaci yayin da aka gabatar da sakamakon karamar hukumar Dala.

Yayin da jam’iyya mai mulki za ta sa ran a samu irin haka a Kano, NNPP na sa ran kuri’un da aka soke ba su kai tazarar da za a samu tsakaninta da APC ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel