Sarkin Yakin Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheka Ana Gobe Zabe A Legas

Sarkin Yakin Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheka Ana Gobe Zabe A Legas

  • Babban daraktan yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar PDP a Jihar Lagos ya ajiye aikinsa daf da zabe ba tare da bayyana dalili ba
  • Tsohon daraktan ya godewa dan takarar bisa damar da ya ba shi na yi ma sa daraktan yakin neman zabe kamar yadda ya bayyana ta cikin takardar ajiye aikin
  • A na shi bangaren, Jandor, dan takarar gwamnan Jihar Lagos a jam'iyyar PDP, ya ce babu wani dan takara da zai janyewa kuma sauyin sheka ba zai dame shi ba saboda dama lokacin hakan ne

Jihar Legas - Dakta Seye Dairo, babban daraktan yakin neman zabe, na dan takarar gwamnan PDP a Jihar Lagos, Dr Abdul-Azeez Olajide Adediran da aka fi sani da Jandor, ya ajiye mukaminsa.

Dakta Dairo, wadda ya sanar da ajiye mukaminsa a wata wasika, bai bayyana wani dalili na daukar matakin ba, rahoton Daily Trust.

Jandor
A Legas: Sarkin Yakin Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheka Ana Gobe Zabe. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ya bayyana godiyarsa ga dan takarar PDP na ba shi dama ya zama babban daraktan yakin neman zabensa.

Jam'iyyar PDP ta jijjiga da ficewar jiga-jiganta da ke komawa jam'iyyar APC mai mulki ko jam'iyyar LP.

An hangi Dakta Dairo wurin taron yan jam'iyyar Labour a Legas

Daga bisani an hangi tsohon daraktan yakin neman zaben da tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Chief Olabode George sun jagoranci sauran mambobin Omo Eko Pataki don komawa tsagin dan takarar jam'iyyar LP, Gbadebo Rhodes-Vivour.

A daya bangaren, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa ranar Alhamis, Jandor ya bayyana cewa babu wani dan takara na wata jam'iyya da ya taba yakin neman zabe irin na shi watanni kalilan.

Ya ce:

''PDP a Lagos ba ta hada kai da kowacce jam'iyya ba, duk yan Najeriya su zabi PDP ranar zabe. Jita-jitar na janyewa wani dan takara karyane.

''Ba mu hada kai da wata jam'iyya ba. A matsayina na dan takarar jam'iyyar, ba zan janyewa kowa ba. Ba dan takarar da ya yi irin aikin da mu ka yi.
''Mun zagaya duk fadin jihar nan kuma mun ga yadda abubuwa su ka chanja daga abin da aka yi a baya. Al'ummar Lagos su yi duba da kyau kan dalilin tsayawarmu takara. Shi yasa aka ce babban zabe, ba zaben cikin gida ba ne.''

Jandor ya yi kira ga magoya bayansa su zabi PDP

Jandor ya kara da cewa zaben 25 ga watan Fabrairu na shugaban kasa, musamman a Lagos, ya kamata ya sa al'ummar jihar su dauki zabe da muhimmanci, ya na cewa ya kamata a zabi gwamna da bai da ubangida wanda ya san Lagos ciki da bai.

A cewarsa:

''Wannan zaben zai bawa al'ummar Lagos iskar yanci. Yanzu lokaci ne da ya kamata mu yi wani abu na daban a Jihar Lagos.

''Jandor, a karan kai na, tun 2016, tare da wasu abokan gwagwarmayata a wannan tafiyar, mun zagaya titunan Lagos mu na wayar da kan mutane, mu na yin duk abin da mu ke ba tare da gajiya ba kuma cikin tsari.
''Mun fahimci bukatunmu. Mu kalli tarihin yan takara da nagartarsu kafin yanke shawara.
''Tabbas, na kula da sauyin sheka daga APC zuwa PDP da kuma daga LP zuwa PDP zuwa ko ma ina ne. Wannan ne lokacin, shi ya sa aka ce babban zabe."

Jigo a jam'iyyar PDP ya fita daga jam'iyya awanni kafin zaben gwamnan jihar Delta

Jigon jam'iyyar PDP a jihar Delta, Dele Omenogor ya fita daga jam'iyyar ana yan awanni zaben gwamna na ranar Asabar.

Omenogor ya koka da cewa gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa ta yi watsi da masarautar Amai da daukakin kasar Ukwuani, hakan yasa ya fice daga PDPn.

Asali: Legit.ng

Online view pixel