Zaben Gwamnoni: Sarkin Kano Ya Aike Da Muhimmin Sako Ana Dab da Zabe

Zaben Gwamnoni: Sarkin Kano Ya Aike Da Muhimmin Sako Ana Dab da Zabe

  • Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero yayi kira ga al'ummar jihar kan muhimmancin zaman lafiya
  • Mai martaba sarkin ya kuma shawarci jami'an tsaro da su nuna ƙwarewa wajen aikin su ta hanyar ƙin goyon bayan kowane ɓangare
  • Sarkin na Kano ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da kada su bari son zuciyar su ya sanya su yi abinda ka iya jefe jihar cikin ruɗani

Jihar Kano- Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, yayi kira ga jami'an tsaro da kada su goyi bayan wani ɓangare a zaɓen gwamnan jihar da na ƴan majalisar dokoki dake tafe.

Mai martaba sarkin ya bayar da wannan shawarar ne lokacin da kwamitin zaman lafiya wanda Abubakar Mahmoud ke jagoranta suka kai masa ziyara a ranar Laraba, a birnin Kano. Rahoton Daily Nigerian

Kara karanta wannan

Kamfen APC Yabar Baya da Ƙura, Ƴan Jagaliya Sun Harbi Tawagar Ɗan Takarar Gwamna, Air Marshal

Aminu
Zaben Gwamnoni: Sarkin Kano Ya Aike Da Muhimmin Sako Ana Dab da Zabe Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Ya bayyana cewa zaman lafiya shine ginshiƙin samun cigaban al'umma, inda yayi gargaɗi ga jami'an tsaro kan buƙatar su nuna cikakkiyar ƙwarewa wajen gudanar da ayyukan dake kan su.

Basaraken ya kuma yi kira ga jam'iyyu da ƴan siyasan dake yin takara a kowane mataki a zaɓen nan da su ba jihar Kano muhimmanci domin kada su je su bari son zuciyar su ya taka rawar gani wajen matakan da zasu ɗauka a siyasance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace a matsayin su na masu imani, yakamata su san cewa shugabanni zaɓin Allah ne wanda tun tuni an ƙaddaro waɗanda za su mulki al'umma, saboda haka akwai buƙatar su ɗauki zaɓe a matsayin kawai cika umurni ne.

Ya kuma shawarci masu kaɗa ƙuri'a da su tabbatar sun bi doka da oda yayin da suke sauke nauyin da ya rataya a kan su na zaɓe, sannan su zaɓi ƴan takarar da suka cancanta waɗanda suka kwanta musu a rai, tare sanyawa a rai cewa akwai rayuwa bayan zaɓe.

Kara karanta wannan

"Na rantse da Allah ban taba ɗaukar sisin Jihar Kaduna ba, wanda ya Ƙaryata Yazo Mu Dafa Kur'ani" - El-Rufai

Kwankwaso: Yadda Na Hango Hadari, Na Yi Wa Buhari Alherin da Ya Ceci Rayuwarsa

A wani labarin na daban kuma, Kwankwaso ya bayyana yadda ya taɓa ceto rayuwar shugaba Buhari.

Madugun na Kwankwasiyya ya bayyana cewa wani haɗari ya hango inda yayi sauri ya ɗauki mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel