2023: Jam'iyyu 5 Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Gwamnan Jihar Yobe

2023: Jam'iyyu 5 Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Gwamnan Jihar Yobe

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya samu wani gagarumin tagomashi ana dab da a fara zaɓen gwamnoni
  • Wasu jiga-jigan jam'iyyun adawa guda uku sun nuna goyon bayan su ga takarar da yake na sake zama gwamnan jihar
  • Jam'iyyun da suka marawa gwamnan baya sun bayyana abubuwan da suka ja hankalin su har suka koma bayan gwamnan a zaɓen dake tafe

Jihar Yobe- Wasu jam'iyyun siyasa guda biyar a jihar Yobe, sun marawa gwamnan jihar, Mai Mala Buni, baya kan takarar da yake na neman sake ɗarewa kujerar gwamnan jihar. Rahoton Daily Trust

Mai Mala Buni, wanda shine ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen ranar Asabar 18, ga watan Maris, yana neman sake komawa kan madafun ikon jihar a karo na biyu.

Mai Mala
2023: Jam'iyyu 3 Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Gwamnan Jihar Yobe Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Jam'iyyun da suka marawa Mai Mala baya a zaɓen na ranar Asabar, sun haɗa da Social Democratic Party (SDP), Labour Party (LP), Action Alliance (AA), All Progressives Grand Alliance (APGA) da Accord Party (AP).

Kara karanta wannan

2023: Kwana 4 Gabanin Zabe, 'Yan Takarar Gwamna 7 Sun Janye Daga Takara

A yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnoni a Najeriya, ƴan takara daban-daban na cigaba da yin ƙulle-ƙullen siyasa domin ganin sun samu nasara a zaɓen dake tafe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban jam'iyyar SDP na jihar Yobe, Abdullahi Bello, wanda yayi magana a madadin sauran jam'iyyun shine ya tabbatar da nuna goyon bayan su ga gwamnan.

Abdullahi Bello ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da suka kira a jiya Talata a Damaturu, babban birnin jihar. Rahoton Parrot Nigeria

Shugaban na jam'iyyar SDP yayi bayanin cewa sun ɗauki wannan matakin ne domin duba mafitar al'ummar jihar Yobe.

Ya bayyana cewa ayyukan alherin da gwamnan ya kwarara a jihar, da yadda ya dawo da zaman lafiya a tsakanin al'ummar ƙauyukan jihar, sune abubuwan da suka sanya su mara masa baya domin sake komawa kan kujerar sa.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Takarar Gwamna 6 Sun Janye Daga Takara Kwana 5 Gabanin Zabe

Yan Takarar Gwamna 7 Sun Janye, Sun Koma Bayan Gwamnan Jihar Legas

A wani labarin na daban kuma, ƴan taƙarar gwamna 7 sun janye daga takarar gwamna a jihar Legas.

Ƴan takarar sun koma bayan gwamnan APC mai neman tazarce a jihar a zaɓen ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng