"Tinubu Ba Shugaban Ƙasar Da Muka Zaɓa Bane", Wata Babbar Fasto

"Tinubu Ba Shugaban Ƙasar Da Muka Zaɓa Bane", Wata Babbar Fasto

  • Fasto Sarah Omakwu ta bayyana cewa Bola Tinubu ba shi bane zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya
  • Babbar faston tayi gargaɗin cewa Tinubu zaɓaɓɓen shugaban ƙasar shugaban hukumar INEC ne da jam'iyyar APC
  • A cewar faston, za a bayyana sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa wanda zai samu nasara ta hanyar sahihin zaɓe

Abuja- Saɓanin abinda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar, wata babbar fasto Family Worship Centre, Abuja, Sarah Omakwu, ta bayyana cewa Bola Tinubu na jam'iyyar APC, ba zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ta bane.

Fasto Sarah lokacin da take magana ga taron mahalarta cocin ta a Wuye, birni tarayya Abuja, tayi zargin cewa an bayyana Tinubu a matsayin wanda yayi nasara ta hanyar da babu gaskiya a cikinta.

Fasto
"Tinubu Ba Shugaban Ƙasar Da Muka Zaɓa Bane", Wata Babbar Fasto Hoto: Independent, APC
Asali: UGC

Pastor Sarah a cikin wani bidiyo ta gayawa taron mahalarta cocin cewa Tinubu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC da kuma jam'iyya mai mulki.

"Mu al'umma muna son mu bayyana cewa Asiwaju Bola Tinubu ba zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mu bane. Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da jam'iyyar APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Za a samu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ta hanya sahihiya kamar yadda dokokin INEC suka gindaya. Daga kaɗa ƙuri'a zuwa sanyawa da ɗorawa akan BVAS, zuwa tattara sakamakon zaɓe da bayyana shi."

A yayin da take cigaba da jawabinta, faston tace tayi amanna cewa za a bayyana a daidai lokacin da ya dace zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da zai ja ragamar ƙasar nan.

"Sannan muna fatan, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mu za a bayyana shi da rana tsaka ba cikin dare ba lokacin mu ke yin barci. Kowa da kowa yana haƙƙi akai ba wai wasu ƴan tsiraru ba." Inji ta

Dino Melaye Ya Bayyana Adadin Biliyoyin da PDP Ta Kashe a Yakin Zaben Atiku Abubakar

A wani labarin na daban kuma, Dino Melaye ya bayyana adadin biliyoyin kuɗin da jam'iyyar PDP ta kashe a wajen yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.

Dino Melaye yana ɗaya daga cikin kakakin yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar na PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel