Yanzu Yanzu: INEC Ta Fara Rabon Muhimman Kayan Aikin Zabe

Yanzu Yanzu: INEC Ta Fara Rabon Muhimman Kayan Aikin Zabe

  • Gabannin babban zaben Najeriya Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fara rarraba kayan zabe a jihar Cross River
  • Za a yi zaben shugaban kasa da na yan majalisun tarayya a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu
  • Don kore shakku, INEC na rabon kayan zaben ne a gaban hukumomin tsaro, jam'iyyun siyasa da kungiyoyin jama'a

Shirye-shirye ya kankama sosai na zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya da za a yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ta fara rabon kayan zabe masu muhimmanci zuwa ofishoshinta na kananan hukuma, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kayayyakin zabe zube a gaban mutane
Yanzu Yanzu: INEC Ta Fara Rabon Muhimman Kayan Aikin Zabe Hoto: Peoples Gazette
Asali: UGC

Wasu ganau a jihar Cross River sun bayyana cewa tuni hukumar INEC ta fara tura kayan zaben zuwa wuraren da ya dace a yau Laraba, 22 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Zafafan Hotunan Kamfen Tinubu/Shettima Na Karshe Da Ya Gudana a Legas

Jami'an tsaro, jam'iyyun siyasa da jama'a sun shaidi yadda ake rabon kayan

Daukacin hukumomin tsaro da suka hada da na yan sanda, NSCDC, SSS, hukumar kula da shige da fice da sauransu suna sanya ido kan yadda ake rabon kayayyakin, Peoples Gazette ta rahoto.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyun siyasa da za su fafata a zaben da kungiyoyin jama'a sun hallara a yayin da ake rabon kayan.

Kwamishinan zabe na yankin, Gabriel Yomere, ya ce sun yanke shawarar gayyatar dukkanin masu ruwa da tsaki domin su shaida yadda ake rabon kayan don kore zargi.

Mista Yomete ya bayyana cewa na'urar BVAS 3,281 aka tanada don amfani da su a rumfunar zabe.

Ya kara da cewa:

"An kuma yi chajinsu ta yadda za su shafe tsawon awanni 48 suna aiki, ba ma tunanin wata matsala ta wutar lantarki dangane da amfani da BVAS.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tsohon Minista Ya Bayyana Yankin Da Atiku Zai Lashe

"A bangaren takardun sakamako, suna nan yadda aka kawo su daga inda suka fito."

Ku tuna cewa a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, hukumar INEC a jihar Edo ta bayyana cewa za ta fara rabon kayan zabe zuwa ofishoshin karamar hukuma a fadin jihar a ranar Laraba.

Kalli bidiyon a kasa:

Malamin addini ya yi hasashen wanda zai lashe zaben shugaban kasa

A wani labari na daban, mun ji cewa wani babban faston Najeriya Prophet Mike Agboola ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ne zai lashe zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel