Shugaban Kasa: Prophet Agboola Ya Yi Hasashe Cewa Atiku Ne Zai Lashe Zabe, PDP Na Murna

Shugaban Kasa: Prophet Agboola Ya Yi Hasashe Cewa Atiku Ne Zai Lashe Zabe, PDP Na Murna

  • Prophet Mike Agboola na cocin Jehovah Power Miracle Tabernacle da ke Ibadan ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar na PDP ne zai lashe zabe mai zuwa
  • Agboola ya ce Atiku da Bola Tinubu na APC na gab da gab yayin da Peter Obi na Labour Party ya yi nisa da su
  • Malamin addinin ya kara da cewar nan take sai Atiku ya yi gaba, sannan ya zama mai nasara a zaben

Oyo - Prophet Mike Agboola shugaban cocin Jehovah Power Miracle Tabernacle da ke Ibadan, jihar Oyo ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na PDP ne zai lashe zabe mai zuwa.

Da yake murnar wannan hasashe, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Dino Melaye, ya wallafa bidiyon jawabin a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 21 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu: Na Ga Obi Yan Sharban Kuka, Malamin Addini Ya Yi Sabon Hasashe Gabannin Zabe

Fasto, Atiku da hannu a sama, Tinubu da Obi rike da abun magana
Shugaban Kasa: Prophet Agboola Ya Yi Hasashe Cewa Atiku Ne Zai Lashe Zabe, PDP Na Murna Hoto: Atiku Abubakar, Peter Obi
Asali: Twitter

Prophet Agboola ya yi hasashen Atiku zai kayar da Tinubu, Obi gabannin zaben shugaban kasa

Koda dai malamin addinin bai ambaci sunayen sauran yan takarar shugaban kasar ba, ya yi bayani da ke nuni ga Bola Tinubu na APC da Peter Obi na Labour Party.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A hasashensa, babban faston ya ambaci APC a matsayin tikitin Musulmi da Musulmi, yayin da ya yi wa Labour Party lakabi da zabin matasa.

APC ita kadai ce babbar jam’iyyar da ke takarar shugaban kasa bisa addini guda a zaben, yayin da ake yiwa Obi kallon zabin matasa, musamman a soshiyal midiya.

Har ila yau, Prophet Agboola ya ce Atiku da Tinubu suna zaune kut da kut yayin da Peter Obi ya yi nisa da su amma sai wani abu ya tura Atiku gaba.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tsohon Minista Ya Bayyana Yankin Da Atiku Zai Lashe

Hasashen Agboola shine na baya-bayan nan da fastocin Najeriya suka yi gabannin zaben, kuma shi kadai ne ya yi hasashen cewa Atiku zai lashe zabe. Ana dai ta hasashe ne tsakanin Tinubu da Obi.

Kalli bidiyon a kasa:

Atiku, Tinubu: “Na ga Peter Obi yana kuma”, malamin addini ya yi sabon hasashe gabannin zabe

Mun kawo a baya cewa Bishop Feyi Daniels na cocin IReign Christian Family ya yi hasashen cewa Bola Tinubu na APC ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023.

A hasashensa, malamin addinin ya kuma bayyana cewa ya ga Peter Obi na LP yana kuka saboda ya fadi zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel