Na Ga Peter Obi Yana Kuka: Cewar Fasto Daniels Yayin da Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben 2023

Na Ga Peter Obi Yana Kuka: Cewar Fasto Daniels Yayin da Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben 2023

  • Bishop Feyi Daniels na cocin IReign Christian Family ya yi hasashen cewa Bola Tinubu na APC ne zai lashe zaben shugaban kasa na 2023
  • Malamin addinin ya bayyana cewa an nuna masa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na LP yana kuka saboda ya fadi zabe
  • A cewar Faston, Atiku Abubakar ba zai taba shugabancin Najeriya ba kuma ya fada masa haka a 2019

Bishop Feyi Daniels, babban fasto a cocin IReign Christian Family, ya yi wasu hasashe cewa za a sanar da dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe mai zuwa.

A wani bidiyo da ya yadu, malamin addinin ya ce an nuna masa Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Tsohon Minista Ya Bayyana Yankin Da Atiku Zai Lashe

Ya kuma ce a wahayin da aka masa, ya ga abun da Tinubu ya sanya yana mai nuni ga yadda yake ta yi.

Fasto da yan takarar shugaban kasa
Na Ga Peter Obi Yana Kuka: Cewar Fasto Daniels Yayin da Ya Bayyana Wanda Zai Lashe Zaben 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku bubakar, Peter Obi
Asali: Twitter

Tinubu na daya daga cikin manyan yan takara a zaben shugaban kasar. Sauran manyan yan takara sun hada da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abun da na hango game da sauran yan takara, Feyi Daniels

Da yake magana kan sauran yan takara a zaben, shugaban addinin ya ce, "Na ga Peter Obi yana kuka, idanunsa sun yi ja da hawaye," yayin da ya ce Atiku ya kasance a fusace saboda ya fadi zabe.

Ya kara da cewar:

"Na fada ma Atiku shekaru 4 da suka wuce cewa ba zai taba zama shugaban kasar Najeriya ba cewa har yanzu yana rubuce a kan dutse, ba zai taba zama ba, don haka babu wani abun damuwa kawai ya je gida ya ajiye kudinsa."

Kara karanta wannan

Yadda Aka So Ayi Amfani da Tinubu Wajen Cin Amanar Buhari a 2019 – Gwamnan PDP

Bishop Daniels yana daya daga cikin malaman addini da dama da suka samu wahayi kan wanda zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@AzeezAd63013799 ya ce:

"Na so wannan bangaren na ga Obi yana kuka""

@big_SAM092 ya ce:

"Hakan ce za ta kasance da sunan Yesu.":

@imabe900 ya ce:

"Insha Allah, zai zo ya wuce."

Ku yi zabe da hankali, ko a sha wahalar shekaru hudu, Shehu Sani ga yan Najeriya

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya bukaci yan Najeriya da su zabi shugabannin da suka cancanta a ranar Asabar ba wai su bi ra'ayi coci ko masallaci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel