Sanata Ya Tona Komai, Ya Jero Manyan Gwamnonin PDP da ke Tare da Tinubu a Boye

Sanata Ya Tona Komai, Ya Jero Manyan Gwamnonin PDP da ke Tare da Tinubu a Boye

  • Orji Uzor Kalu ya fara hango Asiwaju Bola Tinubu zaune a kan kujerar shugaban kasar Najeriya
  • Sanatan Abia ta Arewa ya ce ‘dan takaran APC yana da goyon bayan Gwamnonin Ribas da Abia
  • Ganin karbuwar Tinubu a Arewa da samun goyon bayan Gwamnonin PDP, Kalu ya ce za su ci zabe

Abuja - Orji Uzor Kalu mai wakiltar jihar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, ya bayyana cewa Asiwaju Bola Tinubu ya kama hanyar lashe zabe.

A wata tattaunawa da ya yi da tashar Channels a ranar Litinin, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce Bola Tinubu yana da goyon bayan da zai yi nasara a 2023.

Uzor Kalu ya ce Gwamnonin jihohin Ribas da Abia, Nyesom Wike da Okezie Ikpeazu za su goyi bayan jam’iyyar APC a zaben kujerar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Dab da zabe, Tinubu ya dura a jiharsu, zai yi wani taro da shugabannin Yarbawa

A cewar tsohon na Gwamnan jihar Abia, akwai yiwuwar Bola Tinubu ya karbi shugabancin kasa domin ana matukar kaunarsa a jihohin Arewa.

Baya ga haka, ‘dan siyasar ya ce Tinubu shugaba ne wanda ya san aiki, saboda haka ya cancanta. The Cable ta fitar da labarin hirarsu a yammacin jiya.

TINUBU
Kamfen APC a Borno Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda Tinubu zai lashe zabe

"Idan aka yi lissafi, mu ‘yan APC mun fi yawa. Idan aka duba yawan kasa, a nan ma mu na da yawa. Ba batun a ji ra’ayin jama’a ba ne, wannan bai aiki.
Tinubu ne a kan gaba. Ana son Tinubu a Arewa, kuma daga Kudu maso yamma ya fito, sannan zai samu kuri’u sosai a Imo, Ebonyi, Anambra da Enugu.
Baya ga haka, yana da goyon bayan Gwamna Nyesom Wike na Ribas, don haka za a kai labari.

Kara karanta wannan

Yadda Aka So Ayi Amfani da Tinubu Wajen Cin Amanar Buhari a 2019 – Gwamnan PDP

Gwamnana a nan – Okezie Ikepazu – zai marawa Tinubu baya shi ma. Mutanen mazabata za su ba Tinubu kuri’un – kusan 35% na kuri’un jihar kenan."

Tafiyar G5 a PDP

Ku na da labari akwai Gwamnonin PDP a karkashin jagorancin Nyesom Wike da suka kafa kungiyar G5 saboda zargin maida Kudu saniyar ware a jam’iyyar.

Wadannan Gwamnoni ba su tare da Atiku Abubakar tun da ya zama ‘dan takaran 2023. Tuni Wike ya rufe kofar sulhu da 'dan takaran da jam'iyyarsa ta tsaida.

Seyi Makinde, Samuel Ortom da Ifeanyi Ugwuanyi su ne ragowar Gwamnonin da ke cikin tafiyar G5, da alama a zaben Gwamna ne kurum za su goyi bayan PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel