Sanusi II Ya Yi Magana a Kan ‘Habu na Habu’ da Wanda ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

Sanusi II Ya Yi Magana a Kan ‘Habu na Habu’ da Wanda ya Dace Mutane Su Zaba a 2023

  • Khalifa Muhammadu Sanusi II ya tuno da yadda Gwamnati ta taso shi a gaban saboda sukar APC
  • Sarkin Kano na 14 ya ce an kai karar shi a majalisar dokokin Kano da sunan yana kunyata gwamnati
  • Sanusi II ya nuna ko a lokacin da ya soki shugaba Muhammadu Buhari, bai kira sa ‘Habu na Habu’ ba

Lagos - Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II ya yi wani jawabi inda ya soki yadda al’amura suke tafiya musamman wajen shugabancin Najeriya.

A wannan bidiyo da yake yawo a dandalin Twitter, Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya nuna ba a fadawa shugabanni gaskiya ko a kyautata masu.

A gefe guda, Sarkin ya bayyana cewa shugabanni su kan dauki karon tsana a kan duk wanda ya yi kokarin ya fada masu gaskiya domin ganin an gyara.

Kara karanta wannan

Karya ne: Fadar Shugaban Kasa ta Karyata Zargin El-Rufai da Ganduje

Da aka je aka dawo, Khalifan na darikar Tijjaniya a Najeriya ya ce wadanda suke jin haushin an fada masu gaskiya, su ne suke sukar masu mulki a yau.

Na tuna 2017 - Sanusi II

"Ni na tuna lokacin da Gwamnatin Kano ta ce an bincike ni saboda ina sukar tsarin tattalin arzikin gwamnatin tarayya a shekarar 2017.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har majalisa aka kai ni kara, za a cire ni saboda nayi magana a kan tsarin tattalin arzikin gwamnatin tarayya.
Sanusi II
Muhammad Sanusi II Hoto: @Majeeda_Studio
Asali: Instagram

Yanzu mai gwamnatin Kano take cewa a kan tsarin tattalin arzikin kasar, ai akwai ranar magana, lokacin da aka yi ba lokacin magana ba ne.
Gara ni ban ma ce masa habu na habu ba."

- Muhammad Sanusi II

Tsohon Sarkin yake cewa gwamnati mai-ci ce take caccakar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Tona Abin da Ya Jawo Manya Suke Adawa da Tsarin Canza Nairori

Jaridar Sahelian Times ta ce Sanusi II ya yi wannan magana ne yayin da yake gabatar da karatun littafin Madarijus Salikeen da ya saba yi duk mako.

Wa ya kamata a zaba 2023?

A jawabinsa, an ji Mai martaban ya yi kira ga jama’a suyi tunani da kyau, su zabi shugabanni na kwarai da za su yi alfahari da su, ba wanda za ayi tir ba.

Khalifan ya nuna ba zai ayyana wani ‘dan siyasa da za a zaba ba domin bai da ‘yancin da zai tursasawa ko da yaron cikinsa wanda zai ba kuri’arsa.

Malamai a fagen siyasa

Kun samu rahoto cewa a cikin wadanda suka fito takara na mukamai dabam-dabam zaben bana, akwai wadanda malaman addini ne da suka yi fice.

A yanzu Malamai da Fastoci sun yi tsamo-tsamo a siyasa, su na neman kujerar Gwamnoni a wasu Jihohi, irinsu Sheikh Ibrahim Khaleel a Kano.

Kara karanta wannan

Bayan Jawabin Buhari, CBN Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Abu 3 Kan Sabbin Naira

Asali: Legit.ng

Online view pixel