Hadimin Buhari Ya Tona Abin da Ya Jawo Manya Suke Adawa da Tsarin Canza Nairori

Hadimin Buhari Ya Tona Abin da Ya Jawo Manya Suke Adawa da Tsarin Canza Nairori

  • Bashir Ahmaad ya yi amfani da shafinsa na Facebook wajen yin wasu kalamai masu kama da habaici
  • Hadimin shugaban Najeriyan ya ce masu sukar canza kudi ba za suyi asara ba muddin halal suka mallaka
  • Matashin ya yarda siyasa ta gurbace, yake cewa haka aka yi masa a lokacin zaben tsaida gwanin APC

Abuja - Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen harkokin sadarwa na zamani, Bashir Ahmaad ya jefe wasu maganganu masu kama da habaici.

Da yake magana a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 16 ga watan Fubrairu 2023, Bashir Ahmaad ya kare sabon matakin da mai gidansa ya dauka.

Mai girma Muhammadu Buhari ya amince da canjin manyan takardun kudi, wannan lamari ya jawo masa suka har daga cikin ‘ya 'yan jam’iyyar APC.

Hadimin shugaban kasar ya nuna masu sukar tsarin da sunan kokarin karbo hakkin talakawa, su na yaudarar mutanensu ne don ba haka abin yake ba.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

Ahmaad ya ce wasu masu tir da tsarin sun tara makudan kudin da ba za su iya maida su CBN ba. A maganganunsa, Ahmaad bai kama suna ba.

APC a Oyo
'Dan takaran APC Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da dama daga cikin jama’a suna tunanin cewa wannan kumfar bakin don kwato musu hakki ake yin ta, sai dai gaskiyar magana shi ne suna yi ne don kudaden da suka tara ba za su iya kai wa CBN ba, domin sun san akwai EFCC da NFIU sun zura na mujiya tare da saurare.”

Can kuma sai aka hangi Hadimin Mai girma shugaban kasar yana cewa duk wani mai babatu zai samu kudinsa muddin hukuma tayi binciken da ya dace.

Sako zuwa ga Baba 'Dan Audu

“Baba Buhari ya ce a fadawa su Baba Dan Audu idan kudaden da suke ta kumfar baki a kai na halak ne to su tattara su kai su CBN, idan EFCC da NFIU sun tabbatar da sahihancin su shi kenan za su ji alert.

Kara karanta wannan

Buhari Bai Yi Kokari Sosai a Nan ba, Jigon APC Ya Fadi Bangare 1 da Tinubu Zai Gyara

- Bashir Ahmaad

A cikin maganganu masu harshen damo da matashin ya yi a shafinsa, ya fito yana cewa babu ta yadda za a keta alfarmar abu, sannan kuma ya yi tsarki.

“Ta yaya za ka yi wa abu fyade kuma kayi tsammanin zai ci gaba da zama tsarkakakke?

- Bashir Ahmaad

'Yan siyasar Abuja a Kano

A lokacin da aka ji Gwamnan Kano, Abdulahi Ganduje yana cewa damukaradiyya ta lalace, sai aka ji Bashir Ahmaad ya dauko labarin zaben tsaida gwani.

"Ban tabbatar da cewa demokradiyya ta lalace ba, sai ranar primary election din da nayi takara, kirikiri aka aiko daga sama aka yi mana murdiya a bainar jama’a, wai kawai saboda mu ‘yan siyasar Abuja ne."

- Bashir Ahmaad

Asali: Legit.ng

Online view pixel