Jam'iyyar ADC Ta Janye Daga Neman Shugaban Kasa, Ta Koma Bayan Peter Obi

Jam'iyyar ADC Ta Janye Daga Neman Shugaban Kasa, Ta Koma Bayan Peter Obi

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya samu gagarumin karin goyon baya ana dab da zabe
  • Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa bayan dogon nazari ta yanke shawarar marawa Obi baya ya zama magajin Buhari
  • Nan da kwana ki 5 watau ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023 za'a gudanar da zaben shugaban ƙasa da na majalisun tarayya

Abuja - African Democratic Congress (ADC) ta bayyana goyon bayanta ga ɗan takarar shugaban kasa a inuwar Labour Party, Peter Obi gabanin zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Jam'iyyar ADC ta sanar da wannan matakin da ta ɗauka yayin taron yan jarida a birnin tarayya Abuja ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Peter Obi.
Jam'iyyar ADC Ta Janye Daga Neman Shugaban Kasa, Ta Koma Bayan Peter Obi Hoto: channelstv
Asali: UGC

Daga cikin waɗanda suka halarci taron manema labaran sun haɗa da shugaban ADC na ƙasa, Raphael Nwosu, da kuma babban jigon Labour Party (LP) kuma na hannun daman Obi, Pat Utomi.

Kara karanta wannan

Ta Karewa Atiku, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Arewa Kwana 5 Gabanin Zaben 2023

Rahotanni sun nuna cewa Peter Obi da abokin takararsa, Datti Baba Ahmed, ba su samu halartar wurin ba saboda suna Zariya, jihar Kaduna, inda suka je Ralin kamfe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa suka ɗauki wannan matakin?

Shugaban ADC na ƙasa, Mista Nwosu, ya ce bayan nazari kan masu neman zama shugaban kasa, jam'iyyarsu ta karkare shawari da cewa zata koma gidan Peter Obi.

A kalamansa, Mista Raphael Nwosu, ya ce:

"Mun gamsu cewa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi, da abokin takararsa, Sanata Datti Baba Ahmed, zasu gina shugabanci mai kyau da sauke haƙƙi."

Da yake nasa jawabi a wurin taron, shugaban BoT-ADC, Dr. Mani Ibrahim, ya ce tafiyar Obi/Datti ita ce mafita kuma sun ɗau alkawarin tabbatar da an kai ga nasara a zaɓe, a cewar rahoton Vanguard.

Jam'iyyar ADC ta kasu kashi-kashi sanadin rigingimun cikin gida, wasu mambobin jam'iyyar na goyon bayan ɗan takarar shugaban kasa na ADC, Dumebi Kachikwu.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Kutsa Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10, Bayanai Sun Fito

Haka nan wasu mambobi da ƙungiyoyin magoya baya a ADC suke adawa da zamansa ɗan takarar shugaban kasa a 2023.

Mambobin LP A Arewa Maso Yamma Sun Watsar da Obi

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Arewa Kwana 5 Gabanin Zaben 2023

Mambobin jam'iyyar LP a shiyyar arewa maso yamma sun jingine Peter Obi, sun ayyana cikakken goyo baya ga ɗan takarar shugaban kasa na APC.

Daga cikin masu sauya sheƙar har da yan takarar gwamna, majalisar dattawa da wakilan tarayya da jiga-jigai da shugabannin LP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel