Ministan Shugaba Buhari Ya Siya Fom Na Takarar Gwamnan Jiharsa

Ministan Shugaba Buhari Ya Siya Fom Na Takarar Gwamnan Jiharsa

  • Ƙaramin ministan albarkatun man fetur ya shiga takarar neman gwamnan jihar Bayelsa
  • Abokanan ministan sune suke lale kuɗi daga aljihunan su suka yi karo-karo suka siyawa ministan fom domin yayi takara
  • Timipre Sylva a baya ya taɓa yin gwamnan jihar Bayelsa daga shekarar 2008 zuwa 2012

Tsohon gwamnan jihar Bayelsa kuma ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya shiga takarar neman kujerar gwamnan jihar Bayelsa.

Jihar Bayelsa na ɗaya daga cikin jihohin yankin Kudu maso Kudu wanda aka fi sani da Neja Delta, mai arziƙin ma. fetur. Rahoton jaridar The Punch

Sylva
Ministan Shugaba Buhari Ya Siya Fom Na Takarar Gwamnan Jiharsa
Asali: Twitter

A cewar rahotanni, abokan ministan sune suka siya masa fom ɗin na naira miliyan hamsin (N50m) a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC domin neman takarar kujerar gwamna.

Timipre Sylvia yayi gwamnan jihar Bayelsa daga shekarar 2008 zuwa 2012, sannan daga baya aka bashi muƙamin ƙaramin ministan albarkatun man fetur a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Ta Karewa Atiku, Bola Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya a Arewa Kwana 5 Gabanin Zaben 2023

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za dai a gudanar da zaɓen gwamnan jihar ta Bayelsa ne a ranar 11 ga watan Nuwamban 2023.

Abokanan nasa waɗanda suka siya masa fom ɗin, sun je sakatariyar jam'iyyar APC ta ƙasa a ranar Litinin domin karɓar fom ɗin. Rahoton Blueprint

Timipre Sylva shine jagoran jam'iyyar APC a jihar Bayelsa.

Ministan yana ɗaya daga cikin waɗanda suka siya fom ɗin neman takarar shugaban ƙasa na APC a zaɓen 2023.

Mambobin LP A Arewa Maso Yamma Sun Watsar da Obi, Sun Koma Bayan Tinubu a 2023

A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu wani gagarumin tagomashi a yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Mambobin jam'iyyar Labour Party ta Peter Obi sun yi watsi da tafiyar sa , sun koma bayan Tinubu. Jagoran mambobin da suka watsar da tafiyar Peter Obi, Bashir Ishaq, yace sun shirya tsaf domin tabbatar da Tinubu ya samu nasara.

Bashir ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron manema labarai a madadin ɗaukacin mambobin LP na shiyyar arewa maso yamma, Bashir Ishaq, inda yace za suyi mai dukkanin mai yiwuwa domin ganin Tinubu ya lashe zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel