Bola Tinubu Ya Dira Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10

Bola Tinubu Ya Dira Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10

  • Mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya shiga wurin taron gwamnonin ci gaba da kwamitin NWC
  • Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gayyaci gwamnonin jam'iyar domin tattaunawa kan halin da ƙasa ke ciki
  • Sauya fasalin naira a lokacin kakar zabe ya jefa da yawan mutane cikin kuncin rayuwa lamarin da ya sa gwamnoni suka garzaya Kotu

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyya mai mulki, Asiwaju Bola Tinubu, ya shiga ɗakin ganawar gwamnonin APC da kwamitin gudanarwa karkashin Sanata Abdullahi Adamu.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Bola Tinubu ya isa babbar Sakatariyar jam'iyar APC ta ƙasa da ke Abuja da misalin karfe 5:15 na yammacin yau Lahadi, 19 ga watan Fabrairu.

Taron APC.
Bola Tinubu Ya Dira Wurin Taron Shugaban APC da Gwamnoni Sama da 10 Hoto: APCNigeria
Asali: Facebook

Aƙalla gwamnonin jam'iyyar APC 12 ne suka halarci taron wanda aka fara da misalin karfe 2:35 na tsakar rana yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban APC Ya Shiga Ganawar Sirri Da Gwamnonin APC Kan Rikicin Naira

Da yake jawabin maraba, shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana farin cikinsa bisa ganin yadda gwamnonin suka amsa gayyatarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta rahoto Adamu na cewa:

"Na yi farin ciki da kuka amsa gayyata kuma ga dukkanin alamu akwai sauran waɗanda ke kan hanya zasu ƙariso. Zaku iya tuna ci gaban da aka samu a kwanan nan wanda ya tilasta kiranku taro."
"Bamu son kowa ya hukunta mu bisa la'akari da halin da muke ciki yanzu a ƙasar nan wanda yana shafa wa jam'iyyarmu kashin kaji."
"A ganina ya dace mu kira kowane mai mukami da ya hau mulki a inuwar jam'iyyarmu mu zauna mu fahimci juna kan yanayin da ake ciki. Wannan dalilin yasa na kira ku kuma ina maku maraba zuwa wannan zaman tattaunawa."

An fallasa wasu masu hana ruwa a gudu a Aso Villa

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

A wani labarin kuma mun kawo maku Yadda Wasu Mutum 2 a Aso Rock Suka Sauyawa Buhari Tunani Kan N500 da N1000

Wata majiya mai karfi ta bayyana yadda wani Minista da hadin shugaban kasa suka yi kutun-kutun suka canja wa Buhari tunani kan tsawaita wa'adin tsoffin kuɗi.

An ce shugaban kasa ya yi niyyar tsawaita wa'adin tsoffin kuɗin duka guda uku amma suka masa wani karatu ya gamsu cewa bai dace a ƙara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel