Gwamna Ortom Ya Yanke Shawara, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a Zaben 2023

Gwamna Ortom Ya Yanke Shawara, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a Zaben 2023

  • Gwamna Ortom ya kawo karshen cece-kuce game wanda zai marawa baya ana saura kwana 9 zaben shugaban kasa
  • Ortom, mamba a tawagar G-5 ya jaddada goyon bayansa ga tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi
  • Ya bukaci matasa masu jini a jika su tashi tsaye su tabbata Obi ya ɗare kujera lamba ɗaya a Najeriya

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ƙara tabbatar da goyon bayansa ga ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, Peter Obi.

Gwamna Ortom, mamban tawagar gwamnonin G5 na jam'iyyar PDP ya bayyana Peter Obi a matsayin wanda zai marawa baya ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 2023.

Peter Obi da Ortom.
Gwamna Ortom Ya Yanke Shawara, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a Zaben 2023 Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Mambobin tawagar neman adalci da ake kira G-5 a PDP sun ƙunshi, Nyesom Wike na Ribas, Seyi Makinde, na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abiya, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Ortom.

Kara karanta wannan

2023: Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamna Wike Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Fice Daga PDP

Gwamnonin guda biyar sun nuna fushinsu a lamurra da dama na tafiyar da babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa ciki har da gazawar Iyorchia Ayu na ya sauka daga shugaban PDP.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun nemi Ayu ya yi murabus ne bayan ayyana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a matsayin wanda ya samu nasara a zaben fidda gwanin PDP.

A cewarsu ya zama wajibi a bi abinda kundin dokokin PDP ya kunsa wajen raba manyan muƙaman jam'iyya tsakanin arewa da kudu domin yin dai-daito da adalci.

Yadda gwamna Ortom ya bayyana goyon bayansa ga Obi

A wani bidoyo da ake ya yi a soshiyal midiya wanda Legit.ng Hausa ta gani, an ji Ortom na gaya wa matasa cewa ya zama wajibi su goyi bayan takarar Peter Obi, tsohon gwamnan Anambra.

A bidiyon, gwamna Ortom ya ce, "Ku tashi tsaye ku goyi bayan Peter Obi."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Magana Ta Karshe Kan Yuwuwar Sulhu da Atiku Ana Dab da Zaɓen 2023

Bayan jin wannan kalaman na Ortom, nan take matasan da suka taru a wurin suka fara kiran sunan Obi, Obi suna maimaitawa a tare.

Menene gaskiyar Bidiyon dake yawo?

Da yake tabbatar da inganci da sahihancin bidiyon, Sakataren watsa labarai na gwamnan, Nathaniel Ikyur, ya shaida wa Legit.ng Hausa cewa uban gidansa yana tare da burin Obi.

Mista Iykur ya ce:

"Eh tabbas ya (gwamana Ortom) faɗi haka. Yau abun ya faru a Royal Choice Hotel Makurɗi, taro aka yi na yan Obidient don shirya wa ranar zaɓe."

A wani labarin kuma Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara ta musamman ga gwamna G-5, Seyi Makinde a Ibadan

Mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC, Asiwaju Tinubu, tare da tawagarsa sun ziyarci gwamna Makinde na Oyo, mamban PDP.

Gwamna Makinde na ɗaya daga gwamnonin PDP biyar da suka haɗa G5, waɗanda ke takun saƙa da shugabancin PDP.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Buhari da CBN Suka Jawowa Jam’iyyarsu Bakin Jini

Asali: Legit.ng

Online view pixel