Jam'iyyun Siyasa 5 Sun Rushe Tsarinsu, Sun Koma Bayan Atiku a 2023

Jam'iyyun Siyasa 5 Sun Rushe Tsarinsu, Sun Koma Bayan Atiku a 2023

  • Jam'iyyun siyasa 5 sun bayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar
  • Sun sanar da haka ne a wurin ralin karshe na kamfen jam'iyyar PDP wanda ya gudana yau Asabar a jihar Adamawa
  • Wasu mambobin jam'iyyun siyasa da dama ciki har da APC sun sanar da sauya sheka zuwa PDP a taron

Adamawa - Jam'iyyun siyasa 5 a Najeriya sun rushe tsarinsu baki ɗaya, sun koma cikin inuwar jam'iyyar PDP kana sun ayyana cikakken goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.

Jam'iyyun da suka ɗauki wannan matakin sune, Allied Peoples Movement (APM), Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP), National Rescue Movement (NRM), da kuma African Democratic Congress (ADC).

Ralin PDP a Adamawa.
Jam'iyyun Siyasa 5 Sun Rushe Tsarinsu, Sun Koma Bayan Atiku a 2023 Hoto: Umar M. Goshe
Asali: Facebook

Channels tv ta rahoto cewa jam'iyyun sun sanar da matakin da suka ɗauka a hukumance a wurin ralin karshe na PDP a jihar Adanawa.

Kara karanta wannan

Kwana 7 Gabanin Zaben 2023, Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Takarar Jam'iyyar APC

Da yake jawabi a madadin shugabannin jam'iyyun na ƙasa, shugaban APM na ƙasa, Yusuf Dantele, yace sun yanke shawarin koma wa bayan Atiku ne saboda sun gano ya fi dacewa da mulkin ƙasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa jam'iyyun zasu fafata a zaɓukan gwamnonin, yan majalisun tarayya da na jiha amma a zaɓen shugaban kasa suna tare da Wazirin Adamawa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Bugu da ƙari, jam'iyyar PDP ta karbi masu sauya sheka daga jam'iyyun siyasa daban-daban a wurin ralin ƙarshe cikinsu har da mambobin kwamitin yakin neman zaɓen shugaban kasa na APC.

Ralin wanda ya gudana a filin Ribadu Square ya samu halartar gwamnonin PDP Shida ciki har da gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom, shugaban kwamitin kamfen Atiku/Okowa.

Sauran gwamnonin sune, Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto), Godwin Obaseki (Edo), Bala Mohammed (Bauchi) da mai masaukin baƙi gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Kira Zaman Gaggawa Da Gwamnoninta Gobe Lahadi

Atiku da abokin takararsa gwamna Ifeanyi Okowa na Delta sun karkare kamfe mako ɗaya gabanin zaɓen shugaban kasa wanda aka shirya gudanarwa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Ortom ya yanke shawara ta ƙarshe

A wani labarin kuma Gwamna Ortom Ya Yanke Shawara, Ya Faɗi Wanda Zai Marawa Baya a Zaben 2023

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ɗaya daga cikin gwamnomin tawagar G-5 ya tabbatar da cewa ba zai tallata Atiku Abubakar ba a zaɓe mai zuwa.

Maimakon haka, gwamna Ortom ya bayyana cewa yana goyon bayan takarar Peter Obi na jam'iyar Labour Party a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel