2023: Bola Tinubu Ya Ziyarci Gwamna Makinde Na PDP a Ibadan
- Tsohon gwamnan Legas kuma ɗan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu, ya ziyarci gwamna Makinde a Ibadan
- Wannan ziyara na zuwa ne awanni 24 bayan Tinubu ya gana da gwamna Wike a gidan gwamnatin Ribas dake Patakwal
- Makinde, mamaban G5, ya ce mutanen Oyo sun shirya tsaf su zabi wanda zai zama sanadin haɗin kan Najeriya
Oyo - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar All Progressives Congress, Asiwaju Bola Tinubu, ya ziyarci gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a a gidan gwamnatinsa da ke Ibadan.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Bola Tinubu tare da jiga-jigan jam'iyyar APC da mambobin tawagar PCC suna Ibadan domin halartar gangamin ralin kamfen shugaban kasa.

Asali: Facebook
Sai dai Legit.ng Hausa ta gano cewa APC ta tsara gudanar da ralin a makon da ya gabata ranar Talata amma daga baya ta sauya shawari ta dawo da shi yau Alhamis, 16 ga watan Fabrairu, 2023.
Kwamitin kamfen Tinubu/Shettima ya sauya ranar Ralin ne sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke daga fusatattun 'yan Najeriya kan karancin man Fetur da karancin takardun naira.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wanda mutanen Oyo zasu zaɓa a 2023 - Makinde
Bayan ya karbi bakuncin tawagar, gwamna Makinde ya ce mutanen jiharsa ta Oyo a shirye suka su jefa kuri'unsu ga ɗan takarar da nasararsa zata nuna adalci, daidaito da haɗin kan Najeriya.
Ya ce gwamnatinsa ta yi amanna da sanya bukatun al'umma a matakin farko, inda ya ƙara da cewa, "Masu buga wasan siyasa zasu zo su tafi amma ƙasar mu Najeriya na nan."
Haka nan da yake karin haske kan matsayar tawagar G-5 da kuma rigingimun cikin gida a jam'iyyar PDP, Makinde ya ce:
"Idan muna da zaɓi biyu tsakanin burinmu na kashin kai da kuma haɗin kan ƙasa, zamu zaɓi dunkulewar Najeriya ne a farko."
Ya ce G-5 ta bibiyi zaben fidda gwanin da ya samar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ta yaba da matakin gwamnonin arewa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Gwamna Ortom Ya Yanke Shawara Kan wanda zai wa aiki a 2023
A wani labarin kuma Gwamna Ortom ya tabbatar da cewa yana tare da burin ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi.
Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, mamban G-5, ya bukaci matasa su tashi tsaye su tasa Obi har zuwa kan kujera lamba ɗaya a zabe mai zuwa. A wurin wani taron magiya bayan Peter Obi da suka fi shahara da Obidient, Ortom ya baygana cikakken goyon bayansa ga tsohon gwamnan Anambra.
Asali: Legit.ng