Yadda Aka So Ayi Amfani da Tinubu Wajen Cin Amanar Buhari a 2019 – Gwamnan PDP
- Nyesom Wike ya bada labarin yadda suka lallabi Bola Tinubu ya yi wa PDP aiki a zaben 2019
- Gwamnan jihar Ribas yake cewa Tinubu ya ki yarda ya goyi bayan ‘yan takaran jam’iyyar PDP
- A karshe ‘Dan siyasar ya ce Muhammadu Buhari zai marawa baya a maimakon su Atiku Abubakar
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce Asiwaju Bola Tinubu ya rikewa Shugaba Muhammadu Buhari amana a lokacin zaben 2019.
The Cable ta rahoto Nyesom Wike yana bayanin cewa ya zauna da Bola Tinubu a gidansa, ya roke shi ya goyi bayan Atiku Abubakar ko waninsa.
A wancan lokaci, jagoran na jam’iyyar ya nuna ba zai ci amanar Mai girma Muhammadu Buhari ba, ya gwammace shugaban kasar ya zarce.
Gwamnan na PDP yake cewa shi da kan shi ya je gidan Tinubu domin nemawa Atiku da sauran masu neman takara goyon baya, amma ya ki yarda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya zauna da Tinubu
Mista Wike ya yi zama da ‘dan takaran na APC a yau ne bayan wasu zama da ya yi da shugaban majalisar dattawa da Gwamnan Sokoto a 2017 da 2018.
"Na zo gidanka Bourdillon na kawo ziyara, na fada maka ‘dubi yadda kasa ta ke tafiya; ba za ta yiwu ka bar shugaban nan ya cigaba a 2019 ba.
Sai ka tambaye ni; ‘Su wanene madadin da ake da su?’ Sai na fada maka cewa mu na Atiku Abubakar, mu na da Tambuwal, mu na Bukola.
Sai kayi dariya, ka fada mani ‘gara in tsaya tare da Buhari, idan wadannan ne ku ke da su, to zan tsaya tare da shugaba Muhammadu Buhari.
- Nyesom Wike
Rahoton ya ce Gwamnan ya yi maganar alaka da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Bola Tinubu yana da halayen shugaban da ake bukata.
Wike ya soki Gwamnan CBN
The Nation ta ce Gwamna Wike ya soki yadda babban bankin kasa watau CBN ya ki yin biyayya ga umarnin kotun koli a kan amfani da tsofaffin kudi.
"Ya za ku zama ku na da gwamnati a yau, amma Gwamnan babban banki yana bijirewa kotun koli? Ina ake haka a tsarin damukaradiyya?"
- Nyesom Wike
Abin da ake tsoro - Shehu Sani
A wani rahoto, an ji Shehu Sani yana cewa a lokacin da majalisar tarayya ta amince da kudirin da ya zama dokar canza kudi, ba a fahimci tasirin ba.
Tsohon Sanatan yake cewa ba a wayar da kan mutane sosai ba, sai kwatsam yanzu aka fahimci cewa tsarin yana tasiri a kan rayuwar kowa a kasar.
Asali: Legit.ng