Yanzu Yanzu: Jam’iyyar Labour Party Reshen Kudu Maso Yamma Ta Yi Maja Da APC

Yanzu Yanzu: Jam’iyyar Labour Party Reshen Kudu Maso Yamma Ta Yi Maja Da APC

  • Jam'iyyar Labour Party a yankin Yarbawa ta rushe gaba daya tsarinta ana saura kwanaki 12 zaben shugaban kasa
  • Manyan jiga-jigan jam'iyyar su Peter Obi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasar
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da zaben shugaban kasa inda za a zabi magajin Buhari a tsakanin Atiku, Kwankwaso, Tinubu da Obi

Ondo - Jam'iyyar Labour Party (LP) a kudu maso yamma ta rushe gaba daya tsarinta inda ta yi maja cikin jam'iyyar All Progressives Congress(APC).

Shugaban jam'iyyar LP na kudu maso yamma, Omotoso Banji, shine ya jagoranci shugabancin jam'iyyar wajen rushe tsarinsa a Akure, babban birnin jihar Ondo, jaridar The Nation ta rahoto.

Peter Obi da Bola Ahmed Tinubu
Yanzu Yanzu: Jam’iyyar Labour Party Reshen Kudu Maso Yamma Ta Yi Maja Da APC Hoto: Mr. Peter Obi/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sauran shugabannin LP da suka sauya shekar sun hada da Omowumi Olosola, sakataren LP a Ondo, Sola Alabi da sauransu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya yi wata ganawar sirri da Buhari kan batun Naira

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC ma ya tabbatar da hakan a cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na twitter a ranar Litinin, 13 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama'a sun yi martani

@Nedunaija ya yi martani:

"Mambobi nawa ne a Labour Party?
"Kaso 90 na Obidients ba mambobin Labour Party bane."

@BadmusAdeyemi12 ya yi martani:

"Jam'iyyar LP dai da kuka ce ba su da tsari."

@Ismaeeelmuhd ya ce:

"Lol, tsari ko rashin tsari, talakawa da ke titi za su zabi LP."

@lawaljelilib ya ce:

"Sai me?"

@ogokmc ya ce:

"Ah Ah! Jam'iyyar da bata da tsari tana rushe tsari? Ko dai kun sha wiwi ne? Ku tsaya kan magana daya. LP bata da tari kamar yadda kuka saba fadi..."

@BakrWaziri ya ce:

"Ya Allah ka ga yadda jam'iyyar nan APC ta jefa yawancin yan Najeriya cikin kangin rayuwa, muna addu'a ga Allah ya tsinewa jam'iyyar nan da barayin mutane da suke shugabantar jam'iyyar, Ya Allah ka ji kanmu."

Kara karanta wannan

2023: Kano, Kaduna da wasu jihohi 5 na Arewa duk na Tinubu ne, mataimakin shugaban APC

Duk dan takarar da Wike ya marawa baya ba zai ci zabe ba - Primate Ayodele

A wani labarin kuma, mun ji cewa babban faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashen cewa duk wani dan takarar shugaban kasa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya marawa baya a zaben 2023 ba zai kai labari ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel