Kwankwaso Ya Fadi Abin da Zai Iya Jawo Barkewar Rigima a Sakamakon Zaben 2023

Kwankwaso Ya Fadi Abin da Zai Iya Jawo Barkewar Rigima a Sakamakon Zaben 2023

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya soki hasashen da suke nuna Peter Obi zai lashe zaben shugaban kasa
  • ‘Dan takaran yana ganin sakamakon hasashen yana fitowa a bai-bai, NNPP ya dace ta zama a gaba
  • Kwankwaso ya ce za a iya samun tashin-tashina idan magoya bayan LP suka ga sakamakon zabe

Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a jam’iyyar NNPP, ya soki hasashen zaben shugaban kasar da wasu suke fitarwa.

A wata zantawa da aka yi da shi da gidan talabijin Channels a yammacin Juma’a, Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna hasashen da ake yi ba gaskiya ba ne.

‘Dan takaran shugaban kasar ya koka da yadda ake nuna shi ne zai zo na hudu a zabe mai zuwa, ya ce alkaluman masu hasashen ba daidai yake tafiya ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi: Atiku Ya Fadi Abin da Zai Hana Abokin Takararsa Kai Labari a Zaben 2023

A ra’ayin takaran na NNPP, shi ne wanda ya kamata hasashe ya nuna yana a kan gaba domin kuwa ya samu karbuwa a jihohin da ke Arewacin Najeriya.

Baya ga haka, ‘dan siyasar ya ce jama’a na neman mafita daga APC da PDP a fadin kasar nan.

Mafi yawan hasashen da ake yi na nuna ‘dan takaran jam’iyyar LP, Peter Obi zai lashe zabe, Rabiu Kwankwaso yana ganin a zahiri ba haka abin yake ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Legas Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Abin da Kwankwaso yake gudu

Tsoron da tsohon Gwamnan na Kano yake yi shi ne rikici zai iya barkewa idan sakamakon zabe ya bayyana cewa wanda ake ba nasara bai ci zabe ba.

Tsohon Ministan tsaron ya bada misali da yadda mutane suka tada tarzoma a Arewacin Najeriya bayan jin labarin Muhammadu Buhari ya sha kasa a 2011.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tsage Gaskiya, Ya Faɗi Ɗan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Iya Cin Zaben 2023

Sanata Kwankwaso ya ce a lokacin, masoyan Buhari sun dauka shi zai yi galaba, da suka ga akasin haka, sai aka yi ta kone-kone da kai wa ‘Yan PDP hari.

Jami'an tsaro suyi hattara

Ganin haka ya sa Kwankwaso ya bukaci jami’an tsaro suyi hattara da irin wadannan hasashe da ke fitowa daga wasu wadanda ba su san zahirin lamari ba.

A ra’ayin Kwankwaso, ana amfani da kudi ne wajen sayen sakamakon hasashen, ya kuma yi zargin ana amfani da ra’ayin har mutanen da ke wajen Najeriya.

Tunde ya karyata zargin zagon-kasa

Rahoto ya zo cewa Sabiu Yusuf, wanda ake zargi a Aso Rock da shiryawa Bola Tinubu makarkashiya zai kai karar Alwasn Hassan a Kotu a kan kalamansi.

Hadimin Shugaban Kasar da aka fi sani da ‘Tunde’ ya dauki Lauyoyi bisa zargin kazafi da ya ce Shugaban North-South Progressive Alliance ya yi masa.

Kara karanta wannan

‘Danuwan Tsohon Gwamna Ya Fadawa Duniya Wanda Wike Yake Goyon Baya a Boye

Asali: Legit.ng

Online view pixel