Peter Obi: Atiku Ya Fadi Abin da Zai Hana Abokin Takararsa Kai Labari a Zaben 2023

Peter Obi: Atiku Ya Fadi Abin da Zai Hana Abokin Takararsa Kai Labari a Zaben 2023

  • Kwamitin neman zaben shugaban kasa a PDP ya soki takarar da Peter Obi yake yi a Jam’iyyar LP
  • Daniel Bwala ya ce Obi ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa LP ne saboda ba zai samu tikiti ba
  • Jigon ‘yan adawan ya ce babu wata Jiha a Arewacin Najeriya da Obi zai iya yin galaba a bana

Abuja - Daniel Bwala wanda yana cikin masu magana da yawun bakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a PDP, bai hango nasarar LP.

A hirar da ya yi a shirin gidan talabijin Channels na ‘The Verdict’, Kakakin kwamitin neman takaran ya ce Peter Obi ba zai iya hana su lashe zabe ba.

Daniel Bwala yake cewa ‘dan takaran na shugaban kasa a LP bai yi karfin da zai iya hana Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP yin galaba a zaben bana ba.

Kara karanta wannan

APC da PDP Duk 1 ne: Jigon PDP Ya Share Atiku, Ya Fadi ‘Dan Takaransa a 2023

Duk da ana ganin dinbin matasa su na goyon bayan Obi a zaben shugaban kasa, Mai magana da yawun kwamitin zaben ya ce ba a maganar LP a 2023.

Meya kai Peter Obi LP?

Jagoran jam’iyyar adawar ya ce tsohon Gwamnan na jihar Anambra ya bar PDP ne kurum saboda ya fahimci ba za a ba shi tikitin neman shugaban kasa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Da ya samu tikiti, da bai tafi can (jam’iyyar LP) ba. Ko da ya tafi, bai tafi LP kai-tsaye ba. Ya yi ta neman jam’iyyar da zai shiga ne.
Peter Obi
Peter Obi wajen kamfe Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter
Bari in fada maka wani abu a matsayin masanin shari’a. Peter Obi ‘dan takara ne mai zaman kan shi, ba ‘dan jam’iyyar LP ba ne."

- Daniel Bwala

The Cable ta rahoto Daniel Bwala yana cewa a yayin da Obi ya sauya-sheka zuwa LP, har jam’iyyar hamayyar ta aikawa INEC sunayen ‘yan takaranta.

Kara karanta wannan

‘Dan Takarar Gwamna Ya Yi Hasashen Yadda Zaben Shugaban Kasa Zai Kasance a Kano

A cewarsa, idan aka je wajen INEC aka duba sunayen wadanda suka yi rajista da jam’iyyar LP, ba za a samu sunan ‘dan takaran shugaban kasar ba.

Abin da dokar zabe ta ce kuwa shi ne jam’iyyar siyasa ce ta ke tsaida mai neman takara.

Idan hasashen Bwala da kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar ya tabbata, ‘dan takaran LP ba zai iya nasara a ko jihar Arewa daya a zaben ba.

2023 sai Obi - 'Dan PDP

An ji labari Barista Julius Nnamani yana cewa mutum daya ne kurum daga Kudancin Najeriya wanda ya cancanta da mulkin Najeriya a 2023.

Jagoran na jam'iyyar PDP ya ce a ‘yan takaran shugaban kasa a 2023, Peter Obi ne zai iya maganin bashin da ke kan Najeriya saboda ya yi an gani a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel