PDP ta Saka mu Cikin Jin Kunya: Ayu Yayi Subul da Baka a Kano

PDP ta Saka mu Cikin Jin Kunya: Ayu Yayi Subul da Baka a Kano

  • Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya yi subul da baka inda yace PDP ta kawo abun kunya a kasar nan yayin kamfen
  • Ayu yayi jawabi inda yake sanar da cewa bai dace a sake zaben APC ba saboda jam'iyya ce da ke cike da karya da yaudara
  • Yace Atiku ne yafi dacewa da Najeriya saboda zai kawo tsarikan da zasu inganta rayuwar talakawan Najeriya

Kano - Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na kasa a ranar Alhamis, ya yi subul da baka yayin jawabi a wani kamfen din jam'iyyar a jihar Kano.

Gangamin yakin neman an yi shi ne a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar, jaridar TheCable ta rahoto.

Iyorchia Ayu a Kano
PDP ta Saka mu Cikin Jin Kunya: Ayu Yayi Subul da Baka a Kano. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Yayin jawabi kan dalilin da yasa jam'ar jihar kada su yi kuskuren zaben APC a jihar, Ayu yace:

Kara karanta wannan

Yobe: Atiku Ya Sha Alwashin Dawo da Zaman Lafiya, Bude Iyakokin Nijar da Jihar DOn Assasa Kasuwanci

"PDP ta kawo mana abun kunya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma bayan sakonni kadan, ya gyara maganarsa inda yace APC.

Ayu yace idan Atiku Abubakar, 'dan takarar shugabancin kasa na jam;iyyar, aka zabe shi, zai tabbatar da tsarikan da zasu inganta tattalin arziki.

"Cike suke da karya, babu abinda zasu iya yi wa talakawan Najeriya, Za mu dawo. Shugaban kasanmu Atiku Abubakar, wanda za ku zaba nan da makonni kadan, zai yi maganin komai.
"Za mu tattauna kan tsarikan kuma za mu ga yadda suka taba ku. Za mu tabbatar cewa an kaddamar da tsarin da zai dawo da Najeriya yadda ta ke."

- Ayu yace.

“Mu ya dace mu zama Shugabannin Afrika da ko ina a duniya za a mutunta mu. PDP ta kawo mana abun kunya kuma ba za mu cigaba da barinsu a mulki ba... APC.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

“Ku zabi PDP daga sama har kasa, daga kasa har sama. Atiku matsayin shugaban kasa."

Kwafsarwar Ayu tana daga cikin subul da bakan da 'yan takarar shugaban kasa ke yi.

A ranar 13 ga watan Disamban 2022, 'dan takarar shugaban kasan PDP yayin jawabi a ralin kamfen din Filato, ya roki jama'a da su tabbatar sun zabi A... ina nufin PDP a wannan karon.

Makonni bayan nan, Bola Tinubu, 'dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar APC, yace:

"Allah ya albarkaci PD...APC."

Obasanjo yace yana fatan a yi zabe, kada a dage shi

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa yana tsoron yuwuwar dage zaben 2023.

Ya sanar da cewa, kasashen duniya suna kallon Najeriya ne kuma sun zuba ido su ga irin zaben da za a yi a watannin Fabrairu da Maris

Asali: Legit.ng

Online view pixel