Zaben 2023: Mambobin Jam’iyyar PDP 8,000 Sun Sauya Sheka, Sun Koma APC a Kwara

Zaben 2023: Mambobin Jam’iyyar PDP 8,000 Sun Sauya Sheka, Sun Koma APC a Kwara

  • Kasa da kwanaki 16 kafin babban zaben Najeriya, jam'iyyar PDP mai adawa ta gamu da gagarumin cikas a jihar Kwara
  • Dubban mambobin jam’iyyar su Atiku Abubakar sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ta su Bola Tinubu
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu da 11 ga watan Maris, ne hukumar zabe ta shirya za ta gudanar da zaben bana

Kwara - Akalla mutanen kabilar Bassa 8,000 ne suka sauya sheka daga jam'iyyar People Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Kwara.

Da suke sanar da sauya shekarsu a ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, sabbin mambobin na APC sun sha alwashin zaben Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da sauran yan takarar jam'iyyar a zabe mai zuwa, jaridar Thisday ta rahoto.

Logon APC da PDP
Zaben 2023: Mambobin Jam’iyyar PDP 8,000 Sun Sauya Sheka, Sun Koma APC a Kwara Hoto: Thisday
Asali: UGC

Mutanen Bassa da ke Kwara da suka fito daga jihohi kamar su Kogi, Nasarawa, Filato, Neja, Benue da Abuja manoma ne, kuma sun yadu a garuruwa da dama na jihar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC Ta Samu Babban Ci Gaba da Ka Iya Kawo Wa Atiku Matsala Ana Gab da Zaben 2023

Sarkin Bassa mazauna Kwara ne ya yi wa masu sauya shekar jagora

Masu sauya shekar karkashin jagorancin sarkinsu kuma Aguma Abassa (I), Daniel Shado Zhokwo, sun isa ofishin yakin neman zaben jam'iyyar a ranar Laraba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun kuma samu tarba daga bai ba gwamna shawara ta musamman kan wadanda ba yan jiha ba, Hon. Caleb Ono Bobi da mataimakin shugaban APC a jihar, Alhaji Abdullahi Samari a madadin gwamnan, rahoton The Guardian.

Da yake jawabi a taron, Aguma Abassa, Oba Shado Zhokwo, ya ce sun kawo ziyara ne don sanar da sauya shekarsu daga PDP zuwa APC a hukumance da kuma ayyana goyon bayansu ga Gwamna AbdulRazaq da sauran yan takarar jam'iyyar.

"Mu, mutanen Bassa mun zo nan ne don sanar da kai cewa za mu sauya sheka daga PDP zuwa APC da kuma sanar maka cewa muna ba wannan gwamnati karkashin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq cikakken goyon bayanmu."

Kara karanta wannan

Ana neman matar gwamna: Kotu ta mika dangin Yahaya Bello gidan yari kan badakalar N3bn

Basaraken ya jinjinawa AbdulRazaq kan yadda yake ba wadanda ba yan jiya ba kasonsu a shugabancinsa, cewa gwamnati mai ci ta samu gagarumin nasara a jihar cikin shekaru uku da rabi da suka shige.

Ya bukaci gwamnatin da ta kara baiwa mutanensa tallafi musamman manoma da yan kasuwa, sannan ta sama masu aikin yi da sauransu.

Samuel Weshiri Andrew, wani cikin masu sauya shekar, ya ce ba wai sun sauya sheka saboda samun kudi bane illa saboda sun gamsu cewa gwamnatin ta yi kokari kuma ta cancanci a sake zabarta don kammala kyawawan aikinta.

Ku tanadi katin zabenku don shine makaminku, APC ga masu sauya shekar

Da yake jawabi, Samari ya yabawa mutanen Bassan kan karfin gwiwarsu da shawarar da suka yanke na dawowa cikin tawagar nasara cewa gwamnati da jam'iyyar ba za ta basu da sauran mazauna jihar Kwara kunya ba.

Ya bukace su da su ajiye katin zabensu da kyau gabannin zaben, cewa shine makaminsu na cimma makarfinsu.

Kara karanta wannan

Ta Karewa Obi a Arewa, Yan Takarar Mataimakin Gwamna, Kujerun Sanata Da Majalisar Wakilai Sun Fice Daga LP Sun Koma APC

Tambuwal ya tarbi Tinubu a jihar Sokoto

A wani labarin, mun ji cewa darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, Gwamna Aminu Tambuwal ya tarbi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a jiharsa ta Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel