Siyasa Ba Da Gaba Ba: Bidiyon Yadda Gwamnan PDP, Tambuwal Ya Tarbi Tinubu a Jihar Sokoto

Siyasa Ba Da Gaba Ba: Bidiyon Yadda Gwamnan PDP, Tambuwal Ya Tarbi Tinubu a Jihar Sokoto

  • Jam'iyyun siyasa na ci gaba da gudanar da gangamin yakin neman zabensu a fadin kasar yan kwanaki kafin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya kai kamfen dinsa Sakkwato birnin Shehu
  • Tinubu wanda gwamnoni da jiga-jigan APC suka yi wa rakiya ya samu kyakkyawar tarba a wajen Gwamna Aminu Tambuwal wanda shine DG din kamfen din Atiku na PDP

Sokoto - Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya tarbi dan takarar shugaban kasa na All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu a jiharsa cikin mutuntawa.

Tambuwal shine Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar.

Tambuwal ya tarbi Tinubu a filin jirgin saman Sokoto

Gwamnan na Sokoto yana cikin manyan masu ruwa da tsakin da suka tarbi Tinubu a filin jirgin sama na jihar Sokoto, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sauya Kudi: Da Gaske Gwamnan CBN Na Son Haddasa Rudani a Zaben 2023? Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu

Aminu Tambuwal da Bola Tinubu
Bidiyon Yadda Gwamnan PDP, Tambuwal Ya Tarbi Tinubu a Jihar Sokoto Hoto: Aminu Waziri Tambuwal/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Har ila yau, a cikin bidiyon da jaridar The Nation ta saki, an gano Tinubu wanda ya samu rakiyar gwamnonin da aka zaba karkashin inuwar jam'iyya mai mulki don gudanar da gangamin yakin neman zabensa yana gaisawa da Tambuwal cikin annashuwa da walwala.

Kalli bidiyon a kasa:

A yau Alhamis, 9 ga watan Fabrairu ne jirgin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na APC ya dira jihar Sokoto inda zai tallata kansa da manufarsa.

Za a gudanar da babban zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki inda za a zabi wanda zai gaji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Manyan yan takara a zaben sun hada da Atiku Abubakar na PDP, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC, Rabiu Kwankwaso na NNP da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Gwamna Mai Ci Ya Sauya Sheka Daga PDP Zuwa APC a Wata Jihar Arewa

Wike ba zai tsinanawa Tinubu komai ba a zaben 2023 - Jigon APC

A wani labarin, jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas kuma na hannun damar Rotimi Amaechi, Dr Dakuku Peterside ya ce sam bai san da labarin cewa Gwamna Nyesom Wike na goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ba a zabe mai zuwa.

Peterside ya ce babu abun da Wike zai yi don taimakawa Tinubu a zaben domin dai shi kansa bai da wani tasiri a siyasa a yanzu duk kame-kame yake yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel