Manyan Yan Takarar LP a Jihar Zamfara Sun Sauya SheKa Zuwa APC

Manyan Yan Takarar LP a Jihar Zamfara Sun Sauya SheKa Zuwa APC

  • Dan takarar mataimakin gwamnan jam'iyyar Labour Party a jihar Zamfara ya sauya sheka zuwa APC
  • Jam'iyyar LP ta kuma rasa yan takarar kujerun sanata, majalisar wakilai ta tarayya da majalisar jiha a jihar ta arewa
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake gab da shiga lokacin babban zaben kasar wanda za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu

Zamfara - Dan takarar mataimakin gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Zamfara, Alhaji Sule Dansadau ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), jaridar The Nation ta rahoto.

Haka kuma, jam'iyyar ta Peter Obi ta rasa masu neman takarar kujerun sanata uku da na majalisar wakilai bakwai a jihar.

Masu neman takarar sanatan da suka koma APC sun hada Yahaya Audi Mafara, Zamfara ta yamma; Alhaji Sani Yusuf Danmasami Zamfara ta tsakiya da Injiniya Adamu Yakubu Zamfara ta arewa.

Kara karanta wannan

Sauya Kudi: Da Gaske Gwamnan CBN Na Son Haddasa Rudani a Zaben 2023? Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu

Tinubu da Obi
Manyan Yan Takarar LP a Jihar Zamfara Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/ Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Har ila yau, masu takarar kujerar yan majalisar jiha 14 cikin 19 sun fice zuwa jam'iyya mai mulki a kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abdulaziz Yari ya tarbi masu sauya sheka daga LP zuwa APC

Masu sauya shekar sun samu tarba daga shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan Zamfara na APC, Abdulaziz Yari a wani taro da aka shirya a karamar hukumar Talata-Mafara.

Da yake jawabi a taron, shugaban APC a jihar, Hon. Tukur Umar Danfulani, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Hassan Marafa Damri, ya nuna farin cikinsa a kan wannan shawara da suka yanke, inda ya bayyana hakan a matsayin garabasa ga jam'iyyar.

Damri ya jaddada cewar dole duk wani dan jihar Zamfara mai tunani ya damu da zaman lafiya da daidaitar jihar kuma cewa dole a hada hannu wajen kai jihar gaba.

Kara karanta wannan

Yobe Ta Arewa: Kotun Allah Ya Isa Ta Shirya Yanke Hukunci Kan Shari’ar Lawan Da Machina

Yari ya nuna gamsuwarsa da sauya shekarsu, yana mai cewa sun dauki shawarar da ta dace ta hanyar ajiye muradansu na siyasa da kuma dawowa APC mai mulki.

Ya basu tabbacin cewa APC ce jam'iyyar mutanen Zamfara duba ga yadda ta rike mulki a baya daga rusasshiyar APP, ANPP kuma a yanzu APC.

Dalilinmu na ajiye kudirinmu da dawowa APC

A jawabinsu, dan takarar mataimakin gwamnan da dan takarar sanata mai wakiltan Zamfara ta tsakiya, wadanda suka yi magana a madadin masu sauya shekar, sun fadi dalilinsu na sauya sheka.

Sun ce sun ajiye kudirinsu ne don marawa APC baya saboda zaman lafiya da aka samu bayan sulhu tsakanin tsohon gwamna Abdulaziz Yari da Gwamna Bello Matawalle.

Sun bayar da tabbacin tara magoya bayansu a yayin zabe mai zuwa da kuma zaban yan takarar APC daga sama har kasa, rahoton Daily Post.

Hadimin Tambuwal ya sauya sheka daga PDP zuwa APC a Sokoto

A wani labarin kuma, mun ji cewa hadimin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Abubakar Kwaire ya fice daga PDP inda ya koma jam'iyyar APC mai mulki a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel