Yan Kwanaki Kafin Zaben 2023: Babban Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo Ya Sauya Sheka

Yan Kwanaki Kafin Zaben 2023: Babban Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo Ya Sauya Sheka

  • Yan kwanaki kafin babban zabe, jam'iyyar APC mai mulkin ta hadu da babban cikas a jihar Ondo
  • Wani babban jigon jam’iyyar su Bola Tinubu kuma tsohon kwamishina a jihar Ondo ya sanar da ficewarsa daga APC
  • Fasto Olusegun Aiyerin ya zargi jam'iyya mai mulki da rashin adalci ga wadanda suka yi aiki tukuru don nasararta

Ondo - Ana saura kwanaki 17 babban zaben shugaban kasa, wani tsohon kwamishinan noma a jihar Ondo, Fasto Olusegun Aiyerin, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress(APC).

Ayerin, wanda ya yi ciyaman na karamar hukumar Okitipupa sau biyu, ya sanar da murabus dinsa daga jam'iyyar a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban APC a gudunmar Ilutirun 1 a ranar Talata, 7 ga watan Fabrairu, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamna Sanwo Olu Ya Dakatar Da Kamfe Har Sai Baba Ta Gani, Ya Bada Dalili

Logon APC
Yan Kwanaki Kafin Zaben 2023: Babban Jigon Jam'iyyar APC a Jihar Ondo Ya Sauya Sheka Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar APC

Tsohon kwamishinan ya ce jam'iyyar APC mai mulki a jihar tana karfafawa yan cima zaune gwiwa harda tukwuici yayin da take watsi da masu aiki tukuru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Saboda haka ni Fasto Olusegun Aiyerin ina mai murabus daga matsayin dan APC nan take bayan tattaunawa da ahlina, mabiya da kuma magoya bayana.
"A tuna cewa bayan tattaunawa da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu, yan gwamnoni da wani minista, na yi murabus daga matsayin kwamishinan noma mai ci a jihar Ondo don komawa APC a 2016.
"Bayan na yi duba ga gudunmawar da na bayar a zaben da ya kai ga nasarar gwamnati mai ci, da zabukan da suka biyo baya da kuma sadaukarwar da na yi.
"Na yanke shawarar karshe cewa tsarin jam'iyyar na mayar da alkhairi da alkhairi na da tangarda da nuna banbanci sosai ga wadanda suka yi aiki tukuru yayin da suke karfafa bayar da tukwici ga yan cima-zaune."

Kara karanta wannan

Minista Ya Yi Hasashen Zaben Shugaban Kasa, Ya Fadi Wanda Zai Gaji Buhari

Aiyerin ya bayyana cewa kokarinsa wanda shine hada hannu da sauran jiga-jigan jam'iyyar a jihar don samar da adalci da nuna daidaito bai cimma nasara ba, rahoton PM News.

Zautattun mutane ne za su zabi APC a 2023, PDP

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa zautattun yan Najeriya ne kawai za su zabi jam'iyyar APC a babban zaben kasar mai zuwa.

Ayu wanda ya shawarci yan Najeriya da kada su yi asarar kuri'unsu, ya ce al'ummar kasar sun dandana kudarsu a tsawon shekaru takwas da APC ta yi tana mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel